Mutane da dama sun mutu, sama da motoci 70 sun ƙone sakamakon gobarar tankar mai a Ribas

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga Jihar Ribas sun ce, mutane a dama sun ƙone ƙurmus kana motoci sama da 70 sun ƙone sakamakon fashewar wata tankar mai wadda ta kama da wuta na nan take a yankin Eleme, Jihar Ribas.

MANHAJA ta kalato cewar lamarin ya auku ne a ranar Juma’a da daddare.

Rahotanni sun ce motar ta kama da wuta ne alhali tana ɗauke da mai, lamarin da ya yi sanadiyar ƙonewar motoci masu yawan gaske da ke kusa da kuma haifar da tsaiko a kan hanyar da iftila’in ya auku.

Duk da dai ba a tantance adadin mutanen da suka mutu a gobarar ba, amma dai an ce da yawan mutane sun ƙone a cikin motoci bayan da suka maƙale, wutar kuma ta cim musu.

Wasu sun ɗora alhakin aukuwar iftila’in kan tuƙin gangancin da direban tankar ya yi, da kuma kamfanin da ke aikin gyaran wani sashe na babbar hanya a yankin na Eleme.

Daga bisani, hukumomi tare da taimakon jama’ar gari sun samu nasarar kashe wutar wadda ta yi mummunar mamaya.