‘Yan bindiga sun hallaka kwamandan soji a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

‘Yan bindiga sun harbe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Ɗan Ali dake ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan-ɓauna da aka kai musu.

Majiyarmu ta bayyana cewa, ɓarayin sun yi wa babban jami’in sojin kwanton-ɓauna ne a ƙauyen Malali dake cikin ƙaramar hukumar Ƙanƙara, lokacin da yake tafiya cikin mota ƙirar Hilux don kai wa wasu sojoji ɗauki dake ƙoƙarin fatattakar ‘yan bindigar da suka kawo hari a ƙauyen.

“Kamar yadda ku ka sani Malali na kan hanyar Zangon Pawwa, kuma ‘yan bindiga sun mamaye wannan wuri, saboda haka duk lokacin da aka kawo hari jami’an tsaron dake wurin kan buƙaci sauran jami’ai su kai masu ɗauki daga sansanin jami’an tsaron dake Marabar Ɗan Ali, don haka wannan sabon kwamandan ya kan kai ɗauki wurin cikin gaggawa.” Inji majiyar.

Daily Trust ta rawaito cewa majiyoyi sun ce, an ajiye gawar marigayin, mai muƙamin Manjo a wani asibiti dake Katsina.

“A wannan karon sun nemi a ƙara ma su jami’an soji, ya zo ne da wata mota ƙirar Hilux, madadin tankar yaƙi, wataƙil tankar ba ta samu ba a lokacin.

“Abun takaicin sai kawai maharan da suka kai masa hari, suka harbi motar sannan shima su ka harbe shi a ka.” Inji majiyar.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa, a yayin da ake ƙoƙarin ɗauko gawarsa daga wurin da lamarin ya faru, an yi artabu da muggan makamai tsakanin ‘yan bindigar da jami’an soji, inda jami’in da ya ɗauko gawar shi ma ya samu raunin harbin bindiga.