RSF ta tsananta hare-hare kan birnin al-Fashir na Arewacin Darfur

Sabbin hare-haren dakarun RSF kan birnin al-Fashir na arewacin Darfur ya sanya fargabar sake fantsamar yaƙin Sudan na fiye da shekara guda zuwa yankin wanda ke ɗauke da iyalai aƙalla miliyan 1600 da suka tserewa matsugunansu.

Al-Fashir shi ke matsayin birni mafi girma da baya ƙarƙashin ikon RSF a yankin na yammacin Darfur, duk da yadda mayaƙan na RSF suka mamaye tare da ƙwace iko da dukkanin sauran sassan Darfur wanda ya kai ga zarginsu da aikataa kisan ƙabilanci kan tsirarun ƙabilun da ba Larabawa ba musamman a yammacin yankin.

Dubban fararen hula ne da rikicin na fiye da shekara guda ya raba da matsugunansu ke samun mafaka yanzu haka a arewacin na Darfur, kuma isar rikicin birnin al-Fashir mai tarihi kai tsaye zai sake ta’azzara yakin na Sudan, lura da tasirin yankin wajen ta’azzara rikicin shekarun 2000 mafi muni da ƙasar ta gani a tarihi da ya mamaye iyakar ƙasar da Chadi.

Yawan al’ummar da yanzu haka ke zaune a birnin na al-Fashir ya ƙunshi hadda kusan mutane rabin miliyan da wancan rikici ya tilastawa hijira, lokacin da sojin ƙasar suka yi haxɗaka da dakarun da yanzu suka juye zuwa RSF wajen yaqar ƙungiyoyin ‘yan tawayen da ba na ƙabilun Larabawa ba, sai kuma wasu rabin miliyan da suka sake shiga birnin daga faron rikicin bara.

Tsaffin ƙungiyoyin ’yan tawayen al-Fashir na ci gaba da taka rawar zama ‘yan baruwanmu duk da yadda RSF ke ci gaba da mamaya bayan qwace garin Melit a watan nan wanda ya kange sojin qasar daga iya isa al-Fashir.