Yadda ruftawar bene ta kashe mutum uku a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Wani bene mai hawa biyu ya ruguje ana tsaka da aikinsa a Unguwar Kuntau daura da Kantin M D light, Kano.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a ranar Juma’a inda ya rutsa da masu aikin ginin mutum 12.

Muhammad Usman da aka fi sani da Sharu Mahi yana cikin leburorin da lamarin ya shafa, ya bayyana cewa yana hawa na biyu yana aiki sai ya fito sayayya kafin ya dawo ginin ya rubto.

Ya ce, “Ni ina cikin ma’aikatan rake, kawai na fito saya ina sakkowa ina sakkowa ginin ya ruguje.

“Yan unguwarmu mu bakwai ne yanzu an tono mutum shida saura mutum biyu a iya waɗanda na sani kenan, yanzu ana neman Iroro da wani dattijo da kuma sauran mutum huɗu, sun kama 12 kenan”.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, akwai mutum shida da gini ya danne wanda ake ta ƙoƙarin ganin an ceto su.

Wani maƙwabcin ginin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa, ginin na tsohon Ciyaman ɗin ƙaramar hukumar ne, kuma bulon da aka yi amfani da shi ba mai inganci ba ne.