Ƙarancin Ruwan Sha: Gwamna Buni ya raba wa gidajen sayar da ruwa gas Kyauta

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

A ƙoƙarin nemo mafita dangane da matsalar ruwan sha a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da kewaye, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya baiwa Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jihar rabawa masu gidajen sayar da ruwa kyautar man gas, mako-mako, a Damaturu da kewaye.

Da yake sanya ido dangane da aikin rarraba man gas din a ranar Litinin, Shugaban Hukumar kula da ruwa ta jihar (GM), Engr. Mahdi Zarma ya bayyana cewa wannan yunƙurin ya taimaka wajen rage wahalhalun ruwan tare da tsadar ruwan ga al’umma.

“A kwanakin nan Gwamnati ta ƙara yawan man gas da take rabawa ga injinan rijiyoyin burtsatse sama da 100 da take dasu daga lita 40,000 zuwa lita 60,000 a cikin birnin Damaturu da kewaye, amma duk da hakan mun yi la’akari da cewa har yanzu yankunan da suke da cunkoson jama’a matsalar ba ta kau ba, sakamakon yadda masu gidajen ruwa na sayarwa suke tsawwala farashin ruwan.

“Saboda haka gwamnati ta yanke shawarar tallafa kowane mutum daya da lita 10 ta man gas dake Damaturu, domin ragewa jama’a wahalhalun sayen ruwan. A da masu gidajen sayar da ruwan suna karbar naira 300 a duk kurar ruwa daya, al’amarin da ya tilasta masu tura kurar ruwan sayarwa magidanta kan naira 1000, shima ya danganata da nisan unguwar da kake. Wanda sakamakon wannan canji, mu na sa ran farashin zai rage domin al’umma su samu saukin rayuwam.” Ya bayyana.”

Adamu Abubakar, ɗaya daga cikin masu gidajen sayar da ruwa tare da wani magidanci, Malam Babagana Ali a unguwar Nasarawa a cikin birnin Damaturu, sun bayyana matikar godiya ga wannan hobbasa da Gwamnatin jihar Yobe ta yi domin sauƙaƙa wa jama’a halin da suke fuskanta na ƙarancin ruwan sha.

Bugu da ƙari, Engr. Zarma ya kara da cewa, sama da gidajen sayar da ruwa 100 suka ci gajiyar tallafin man gas din, a ƙoƙarin Gwamnati na shawo kan matsalar, a Damaturu da kewaye.