Ɗan majalisar Birnin Kano ya raba wa mutane 100 tallafin jari a mazaɓar Ɗan’agundi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ɗan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birnin Kano Hon. Ambasada Sarki Aliyu Daneji ya yi rabon tallafin jari ga al’ummar mazaɓar Ɗan’agundi.

Da yake bayani game da tallafin ɗan majalisar Hon. Ambasada Sarki Aliyu Daneji ya ce tallafin na mutum 100 ne kuma da yardar Allah nan gaba za su sake dawowa su baiwa wasu duk waɗanda ba su samu a wannan karo ba su kwantar da hankalinsu har sai ya kai kowa ya dangwali romon dimukraɗiyya.

Ya ce daga cikin ayyuka da ya gudanar cikin watanni 9 da zuwansu majalisar Jihar Kano cikin ikon Allah ya ba shi dama wajen ɗaukar mutum 105 ya kaisu makarantar Legal akwai mutum 120 da aka Kai makarantar share fagen shiga jami’a ta CAS. Akwai waɗanda aka kai makarantar tuƙin jirgin sama dana ruwa da na ƙasa.

Hon. Ambasada Sarki Aliyu Daneji ya ƙara da cewa akwai aikin lafiya da suka yi na aikin yanar ido ga mutum 500 dana sa haƙori na mutum 450 tare da gina masallaci a unguwar Gandun Albasa sannan za a soma aikin magudanan ruwa da sanya intaloki a dukkan mazaɓu na Ƙaramar Hukumar Birnin.

Ambasada Sarki Aliyu Daneji ya gode wa al’ummar mazaɓar Ɗan’agundi da na dukkan mazaɓun qaramar Hukumar Birnin Kano bisa irin haɗin kai da goyon baya da suke ba shi.

Tun da farko a taron shugaban ƙaramar Hukumar Birnin Kano Hon. Baba Chilla ya bayyana jin ɗaɗinsa bisa rabon tallafin da ɗan majalisar jiha mai Birnin Kano Sarki Aliyu Daneji ya yi ga mata da matasa a Ɗan’agundi.

Ya ce wannan irin ayyuka ne da aka yi wa al’umma alƙawari lokacin da ake yaƙin neman zaɓe kuma cikin hikimar Allah da baiwarsa da yardarsa ya kawo shi wannan mazaɓa domin gudanar da wannan aiki na alkhairi.

Hon. Bashir Chilla ya ja hankalin waɗanda suka amfana da tallafin su yi amfani da shi wajen gudanar da ƙananan sana’o’i domin su amfani kansu da sauran al’umma da suke tare da su.