Kawar da ciwon hanta kafin 2030

A baya-bayan nan ne ƙasashen duniya suka gudanar da bikin ranar yaƙi da cutar ‘Hepatitis’ wanda ake kira da ciwon hanta a Hausance, domin ƙara wayar da kan jama’a game da wannan mummunar cuta da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Hepatitis ya kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka haɗa da; Hepatitis A, da Hepatitis B, da Hepatitis C, da Hepatitis D, da kuma Hepatitis E.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta nau’in B da C a duniya. A yayin da ciwon hanta nau’in B kawai ke kashe rayuka 900,000 duk shekara.

Har ila yau, hukumar lafiyar ta ce, kaso 10 cikin 100 ne kawai na masu fama da cutar hanta nau’in B da kuma kaso 19 cikin 100 na masu fama da ciwon hanta nau’in C suka san suna ɗauke da cutar.

Wannan na nuni da miliyoyin mutane da ke fama da ciwon hantar amma basu sani ba, kuma hakan na faruwa ne saboda ƙarancin zuwa asibiti domin gwajin ciwon hanta akai-akai.

Haka nan, kaso 42 cikin 100 ne kawai na yaran da ake haifa a faɗin duniya suke iya samun allurar rigakafin ciwon hanta nau’in B bayan haihuwarsu. Saboda haka hukumar ke sake jaddada kira game da yaɗuwar cutar daga uwa zuwa jariri cewa, ya kamata dukkan jarirai su sami rigakafin ciwon hanta nau’in B bayan haihuwarsu.

Sai dai kuma bincike ya nuna cewa Hepatitis A, Hepatitis B, da kuma Hepatitis C su ne suka fi wanzuwa tsakanin mutane.

Alamomin ciwon hanta sun haɗa da; Ciwon ciki, zafin jiki, amai, tashin zuciya, kasala, baqin fitsari, idanuwa su yi kalar ɗorawa da jiki, ƙaiƙayin jiki, bahaya kore.

Ga ɗan bayani akan cutar Hepatitis A,B,C,D,E a qasa:

Hepatitis A:

Ana kamuwa da qwyar cutar Hepatitis A ne ta hanyar gurvataccen abinci ko ruwan sha wanda ya gaurayu da kashin wani mai ɗauke da cutar, wanda ƙwari ke yaɗawa, sannan ya fi yaɗuwa ne a ƙasashen da tsaftar muhalli ke da ƙaranci.

Hepatitis B:

Ƙwayar cutar hepatitis B cuta ce ke haddasa wannan rukuni na ciwon hanta, wanda ke yaɗuwa a cikin jinin mutumin da ya kamu da ita. Ana kamuwa da shi ne idan aka sanya wa mutum jinin mutumin da ke ɗauke da shi, yin amfani da allura ko reza, ko wasu ƙarafa masu ɗauke da ƙwayar cutar. Haka zalika, ana ɗauka daga uwa zuwa ɗanta, da kuma saduwa da wanda ke ɗauke da cutar.

Binciken lafiya ya nuna cewa cutar hanta wato Hepatitis B ta zamo cutar da ke kisa a voye.

Masana harkar lafiya sun ce cutar ta fi kisa fiye da cutar zazzavin cizon sauro a shekara. Binciken ya ce, kimanin mutane miliyan 257 ne ke fama da cutar samfurin ‘B’ a duniya, kuma Nijeriya na daga cikin ƙasashe biyar da ke da kashi 60% na masu fama da wannan cutar. An ware ranar 28 ga watan Yulin ko wace shekara a matsayin ranar ciwon hanta ta Hepatitis.

Hepatitis C:

Ana kamuwa da shi ne ta ƙwayar cutar Hepatitis C. Yana yaɗuwa ne ta hanyar sanya wa mutum jinin wanda ke ɗauke da ita.

Hepatitis D:

Ana kamuwa da shi ne ta ƙwayar cutar Hepatitis D. Yana shafar mutumin da ya riga ya kamu da cutar hepatitis B ne, domin yana buƙatar kwayar cutar hepatitis B kafin ya iya tsira a jikin mutun. Yana yaɗuwa ta hanyar sanya wa mutum jinin mai ɗauke da ita da kuma saduwa da wanda ke ɗauke da cutar. Daɗewar wannan cuta na iya sa mutum kamuwa da cutar dajin hanta.

Hepatitis E:

Ana kamuwa da shi ne ta ƙwayar cutar hepatitis E. Sannan akan kamu da shi ne ta hanyar cin ɗanyen naman alade. Wannan baya daɗewa a jikin mutum, sannan baya buƙatar kowani magani, amma ya kan munana a cikin wasu mutane.

Wasu daga cikin matakan kariya sun haɗa da:

  • Tattaunawa da likita kan ɗaukar alluran rigakafin ciwon hantar.
  • Kada a yi amfani da allura, reza ko burushin goge baki da wani ya ke amfani da su.
  • Ga masu juna biyu, tattauna da likita kan yadda za a kare yaɗuwar cutar zuwa jariri.
  • A yi amfani kaɗai da abubuwan yanka jiki (kamar askar aski ko askar tiyatar likita) da aka tsabtace su daga dukkan qwayoyin cuta.
  • A lizimci amfani da kwaroron roba (condom) ko da yaushe yayin saduwa da wanda ke ɗauke da cutar ko haɗarin kamuwa da cutar.
  • Idan zai yiwu, a zaci shan qwayar magani maimakon yin allura.

A cewar Darektan Hukumar ta WHO a Nahiyar Afirka, Dakta Matshidiso Moeti, a wani saƙo na bikin ranar yaƙi da cutar Hepatitis ta duniya ta 2022, ya sanar da cewa, cutar hanta ita ce ke da alhakin mutuwar mutane kusan 125,000 a Afirka duk shekara, duk da samun magani.

Ya yi kira ga dukkan gwamnatocin Afirka da su himmatu wajen karkatar da kulawa zuwa matakin kiwon lafiya na farko, ta yadda za a samu sauqin jinya ga kowa, ba tare da la’akari da inda ya ke zaune ba.

Ya kuma buqace su da su sanya fifiko kan kuɗaɗe don magance wannan barazanar lafiya da za a iya maganceta. Ya buƙaci qasashen Afirka da su samar da hanyoyin da za su iya bi, tsarin kiwon lafiya don tantance gudummawar jini ga cutar hanta, da tabbatar da cewa an yi amfani da sirinji sau ɗaya kawai kuma a zubar da shi a shara, domin waɗannan su ne manyan abubuwan da ke taimakawa wajen yaɗuwar cutar hanta. Ya buƙaci al’ummar Afirka da su je a yi gwajin cutar da kuma kula da su.

An bayyana Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da yawan masu ɗauke da kwayar cutar a cikin ƙasashe 47 na Afirka. Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa, kimanin kashi 12 cikin 100 na al’ummar Nijeriya miliyan 200 da aka kiyasta suna fama da cutar hanta na kullum wato Hepatitis B, yayin da kashi biyu cikin 100 na fama da cutar hanta ta C.

Kuma yayin da bincike ya nuna cewa Nijeriya tana da tsarin kula da cutar hanta ta ƙasa da kuma wani shiri mai muhimmanci na cutar hanta, an ce yawan allurar rigakafin cutar hepatitis B ya kai sama da rabi, kashi 58 cikin 100 a ƙasar, inda har yanzu mutane da dama ba su san cutar ba saboda rashin kulawa da dalilai daban-daban kamar rashin bayar da rahoto.

Don haka wannan jarida ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara wayar da kan jama’a game da cutar, tare da ƙarfafa gwiwar jama’a da su je a yi gwaje-gwaje, idan kuma ana so a yi musu magani.

Ya kamata gwamnatin tarayya ta kuma samar da kayan aiki tare da raba hanyoyin tantance cutar hanta da kuma kula da cutar hanta daga asibitocin tsakiya zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta yadda zai iya isa ga kowa.