Masu kwaɗayin kujerar shugabancin Nijeriya su rungumi ƙaddara, Tinubu sai ya yi takwas – Ganduje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai ci gaba da zama shugaban Nijeriya har bayan 2027.

Ganduje ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga dandazon magoya bayan Jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Ganduje ya ƙara da cewa tun ba a kai ko’ina ba jam’iyyun adawa sun fara kermar tsoron yin gaba da gaba da APC a zaɓuka masu zuwa bayan ɗan karan kayen da suka sha a zaɓen 2923.

“Jam’iyyar NNPP sun fi duk jam’iyyun kiɗimewa. Sai tsalle-tsalle suke yi ba su nan ba su can. Kuma wai fa duk shirin 2027 su ke yi.

“Abinda zan faɗi musu kuwa shine kujerar shugaban ƙasa ta Tinubu, ba a buqatar canja ta. Saboda tun yanzu sun sha ƙasa. Kuma ku sani cewa muna sane da waɗanda ke ƙoƙarin kawo ruɗani a jam’iyyarmu, kawai don a riƙa cewa an samu ɓaraka.

“Su sani muna nan ta ɗaure tamau kamar yadda aka san mu, ba bu abinda ya girgiza ko yake bamu tsoro. Su je can su cigaba da ƙulla makircinsu mu kuma nuna nan muna ƙara shiri.

“Idan da za ku yi nazarin yadda abubuwa ke faruwa a jihar Kano za ku ga cewa ko su kansu jam’iyyar adawa a rabe suke.”