Gwamna Abba Kabir ya ƙaddamar da aikin gadar sama da ƙasa ta Tal’udu

  • Nan gaba kaɗan gadar Ɗan’agundi za ta biyo baya, inji gwamnan

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ƙaddamar da aikin gadar ƙasa da sama da aka fara aikinta a ranar Asabar.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan aiki na da nasada da alqawarin da aka ɗaukar wa al’umma yayin da suke yawon yaƙin neman zaɓen shekarar 2023 da ya gabata.

Maigirma gwamna Abba ya ƙara da cewa wannan aiki da zai gudana yana da nufin kawo sauƙi ga al’ummar ciki da wajen jihar musamman masu shigowa don gudanar da harkokin kasuwanci.

“Kamar yadda muka yi wa al’umma alƙawari za mu kawo masu ayyukan raya ƙasa da ci gaba don dogaro da kai, shi ya sa muka fara da wannan gada ta Tal’udu dake cikin ƙaramar hukumar Dala.”

“Kun sani cewa tunda muka zo matsayin da muke ayau na shugabancin al’ummar jihar Kano, mun yi ayyuka da yawan gaske dan taimakon jama’armu da ciyar da jiharmu gaba.

Gwamna Abba ya kuma bayyana ƙudurinsa na cigaba taimawa matasa da sauran al’umma da ayyukan yi da sauran hanyoyin dogaro dakai bisa kokarin su wajen tsayawa kai da fata dan tabbatuwar wannan gwamnati.

Haka kuma gwamna ya bayyana cewa za suyi duk mai yuwuwa wajen ganin yan kwangilar sun yi aikin su cikin lokaci da aka diba dan kammala aikin.

“A nan muna san sanar da Al’ummar jihar Kano cewa bamu fara wannan aiki ba har sai ɗa muka tabbatar mun shirya.

Gwamna yakuma roki al’umma musamman wadanda suke zaune a wannan yanki dasu bada goyon baya don ganin wannan aiki ya kammala cikin sa’a.

Alhaji Abba Kabir ya kuma ƙara da cewa a nan bada jimawa ba shi ma aikin gadar sama da ƙasa na titin Ɗan’agundi zai soma kamar yadda akayi alƙawari ga al’ummar jihar Kano lokacin da ake buƙatar su sa hannun jarinsu da ya taimaka wajen kafuwar wannan gwamnati tasu.