Nijeriya ba ta shirya kafa ‘yan sandan jiha ba – Sufeto Janar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sufeto Janar ɗin ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya bayyana cewa Nijeriya ba ta kai ga ta kafa ‘yan sanda jiha ba wanda gwamnoni a jihohi ke da iko da.

Egbetokun ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron tattaunawa kan kafa ‘yan sandan jiha wanda kwamitin majalisar wakilai kan duba kundin tsarin mulkin ƙasa ya shirya.

Ya ce rundunar ‘yan sandan ƙasa ba ta amince da hakan ba, amma kuma ta na rokon Majalisar Ƙasa ta duba yiwuwar ƙara kason ‘yan sanda a kasafin kuɗin ƙasa.

Ya kuma ce kafa ‘yan sandan jihohi zai ƙara ta’azzara rikicin ƙabilanci da ake fama da shi a Nijeriya. Jawabin ya ci karo da rashin amincewar masu sauraro da inda suka yi wa Okolo ihu, suna cewa ba su yarda ba.

Matsayin Sufeto Egbetokun ya sabawa matsayin da Tinubu ya bayyana a bainar jama’a game da kafa ‘yan sandan jihar.

Idan ba a manta ba, Shugaba Tinubu tare da wasu gwamnonin Nijeriya na buqatar a kafa ‘yan sandan jihohi a Nijeriya ta yadda kowacce jiha za ta riƙa iko da jami’an ‘yan sandan ta.

Sai dai kuma wasu da dama na ganin yin hakan zai ƙara ruruta kiyayya tsakanin mutanen Nijeriya ganin cewa har yanzu akwai rashin yadda da juna da kuma rikice-rikice na addini da na ƙabilanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.