Jam’iyyun siyasa na shirin ƙalubalantar sojojin Mali a gaban kotun ƙoli

Ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun siyasa a Mali sun buƙaci kotun ƙoli kan ta umarci gwamnatin sojin ƙasar da ta dakatar da haramcin da ta yi game da gudanar da harkokin siyasa. 

A wata sanarwa da suka fitar, ƙungiyoyin fararen hular da jam’iyyun siyasa da ke adawa da umarnin Sojojin, sun yi ƙorafi ga babbar kotun ƙasar ta Mali, suna neman a soke hukuncin da suke ganin take haƙƙin ɗan adam ne.

Tun a shekarar 2021 ne sojoji a Mali suka yi juyin mulki karo na biyu, inda suka yi alƙawarin gudanar da zaɓe a watan Fabrairun da ya gabata tare da maida mulki ga farar hula tun a watan Maris.

Sai dai mahukuntan ƙasar sun ɗage zaɓen a watan Satumbar bara saboda wasu dalilai, yayinda har zuwa yanzu ba su sanar da dalilin gaza zaɓen na watan Maris ba.

Tashe-tashen hankula a ƙasar ta Mali na ci gaba da ƙaruwa, sakamakon gaza cika alƙwarin gudanar da zaɓe da sojojin da ke mulkin ƙasar su ka yi a baya.

Lamarin da masu fafutuka ke kallon sa a matsayin koma baya ga dimokraɗiyya a ƙasashen yammaci da tsakiyar Afirka, inda aka yi juyin mulki takwas cikin shekaru huɗu da suka gabata.