Gwamnan Sakkwato ya tuɓe rawanin hakimai 15

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Sakkwato ta sallami hakimai 15 bisa zargin su da taimakawa rashin tsaro, satar filaye da sauran laifuka.

An sallami hakimai 9 daga muqamansu bisa zargin su da rashin biyayya da taimakon rashin tsaro da satar filaye da kuma karkatar da dukiyar jama’a da rashin ɗa’a.

Waɗanda aka sallama sun haɗa da hakiman Uguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, llela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da kuma Hakimin Gyawa.

Gwamnatin jihar ta kuma sauke wasu hakimai shida da tsohuwar gwamnatin jihar ta naɗa.

Abubakar Bawa, Sakataren yaɗa labarai na Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa an sauke hakiman shida ne saboda yadda aka naɗa su bisa ga la’ida da kuma ƙin amincewa da mutanensu suka yi.

Sun haɗa da hakimin Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun ’Yar Tsakkuwa, da kuma Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Torankavwa.

Bawa ya ƙara da cewa “An yaba da ƙararrakin da suka shafi Hakiman Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi don ci gaba da bincike.”

Sai dai Sarkin Yakin Binji, babban mai ba da shawara a Majalisar Suktanate an mayar da shi Nabunkari yayin da Hakimin Sabon Birni ya kai Gatawa.

Bawa ya lura cewa, an bar wasu hakimai bakwai a kan kujerunsu da suka hada da Alhaji Aliyu Abubakar III (Shugaban Sakkwato); Alhaji Ibrahim Dauki Maccido (Barayar Zaki); Abubakar Salame (Sarkin Arewan Salame) da Aminu Bello (Sarkin Yamman Balle).

Sauran su ne Mahmoud Yabo (Sarkin Gabas Dandin Mahe); Muntari Tukur Ambarura (Sarkin Gabas Ambarura) da Malam Isa Rarah (Sarkin Gabas Rarah).

Hakazalika, Hakiman Tsaki da Asare suma an rike su yayin da aka mayar da Abdulkadir Mujeli a matsayin Sarkin Rafin Gumbi.