Tsananin zafi: An buƙaci mutane su dauki matakan kariya na kiwon lafiya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A halin da ake ciki na yanayin tsananin zafi, an yi kira ga al’umma da su ɗauki matakan kariya na kiwon lafiya domin kare lafiyarsu daga faɗa wa haɗari.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi kiran a cikin wata sanarwar manema labarai da ma’aikatarsa ta fitar ranar Alhamis wadda aka raba wa manema labarai.

Sanarwar wadda ta sami sa hannun Ibrahim Abdullahi, Dakta Labaran ya ce yanayin zafin da ake ciki ya fara ne tun daga watan Maris na wannan shekara, wanda ya sanya ƙaruwar zazzaɓi da mace-mace, ya ƙara da cewa tun daga lokacin ma’aikatar lafiya ta shiga binciken gano haƙiƙanin abin da ke faruwa.

Kwamishinan ya yi nuni da cewa al’ummar Kano sun san waɗannan watanni guda uku – Maris, Afrilu da Mayu, har ma da farkon watan Yuni watanni ne na ta’azzarar zafin rana wanda hakan ke janyo abubuwa masu yawa da suka haɗa da ƙaruwar zazzaɓin cizon sauro da cutar sanƙarau.

“Idan an lura za a ga watanni uku zuwa huɗu da suka gabata sauro ya yi ƙasa sakamakon yanayin sanyi, amma yanzu ya ƙaru saboda tsananin zafi; zafin ya ta’azzara zuwa matakin da zai iya taɓa ƙwaƙwalwa ko hanta ko kuma ƙoda, wanda kowane ɗaya daga cikin waɗannan sassa idan zazzaɓin cizon sauro ya taɓa yakan iya janyo halaka.

“Tsananin zafi a jihar Kano yanzu ya kai mizanin 43 zuwa 45, sannan iskar da ke yawo busasshiya ce, babu danshi a cikinta. Wannan yanayi kan haddasa tsagewa a wata kafa a cikin hancin mutum da idan ya shaƙi ƙwayoyin cutar da ke haifar da cutar sanƙarau, kuma suka shiga cikin ƙwaƙwalwa suna iya haddasa masa cutar sanƙarau.

“Hakan ne ya sa ake ganin zazzaɓi, tsananin ciwon kai, suma da rasa rai na ƙaruwa”, in ji Dakta Labaran.

Ya kuma yi nuni da cewa tsananin zafin, har ila yau, na janyo cutar shanyewar ɓarin jiki saboda ƙarancin jini da ruwa da ake samu a jikin mutum sakamakon tsananin zafin, wanda kan iya haifar da matsalar ƙwaƙwalwa, musamman ga waɗanda suka manyanta, da masu aikin ƙarfi.

Daga nan ya shawarci mutane da su guji barin sauro yana cizon su ta hanyar kwana a gidan sauro, ko sanya raga a ƙofofi da tagogi ta yadda sauro ba zai iya shiga ɗaki ba, ko yin amfani da sinadarin kashe sauro na feshi ko na shafa a jiki ta yadda sauro ba zai sauka a jiki ba.

Dakta Labaran, ya kuma shawarci mutane cewa da zarar sun ga alamun zazzaɓin cizon sauro a kai mutum asibiti domin a ba shi magani, yana mai jaddada cewa kada a bari sai ya kai matsayin da ya yi masa illar da ba za a iya komai a kai ba.

Game da cutar Sanƙarau kuwa, kwamishinan ya ja hankali mutane da su kauce wa cunkoso a ɗakunan taro da na kwanciya musamman waɗanda babu iska sosai, ya ƙara da cewa da zarar an ga mutum yana fama da zazzaɓi da ciwon kai, a hanzarta kai shi asibiti a duba don a tabbatar ba cutar sanƙarau ba ce.

Ya kuma buƙaci likitoci da idan mutum ya zo asibiti ɗauke da zazzaɓi a tsaya a duba shi sosai don a tabbatar ba cutar sanƙarau ba ce kada kawai a zaci zazzaɓin cizon sauro ne, inda ya tsoratar da cewa idan an bar cutar sanƙarau ta kwana ɗaya zuwa biyu a jikin mutum tana iya janyo halaka.

Kazalika, ya ja hankalin jama’a, musamman masu aikin ƙarfi, da su guji shiga rana, sannan su yawaita shan ruwa da samun hutu sosai domin gujewa kamuwa da mutuwar ɓarin jiki, yana mai tabbatar da cewa haka zai taimaka ƙwarai da gaske wajen kare mutum daga afkawa cikin matsala.