Fursunoni 118 sun tsere bayan da ruwan sama ya lalata gidan yari a Neja

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga garin Suleja a Jihar Neja sun ce, aƙalla fursunoni 119 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a garin a daren Laraba wanda ya lalata wani sahshe na gidan yarin.

Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari na yankin FCT, Adamu Duza ya tabbatar da aukuwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar Alhamis.

Ya ce, “Ruwan sama mai ƙarfi da aka yi na awanni masu yawa a ranar Laraba, 24 ga Afrilun 2024, ya haifar da akasi a matsakaicin gidan yarin Suleja, Jihar Neja.

“Ya lalata wani sashe na ginin gidan yarin wanda ya haɗa da kantagar da ke kewaye da ginin, lamarin da ya yi sanadiyar tserewar fursunoni 118 daga gidan yarin.”

Ya ƙara da cewa, faruwar haka ke da wuya hukumar ta ɗauke matakin sake kamo tserarrun fursunonin wanda kawo yanzu ta samu nasarar sake kamo 10 daga ciki, sannan tana kan farautar ragowar.

Jami’in ya ce, duba da gine-gine na tun zamanin Turawan Mulkin Mallaka ne, don haka sun tsufa, kuma hukumar na ƙoƙarin ganin an bi dukkan gine-ginen gidajen yarin da suka tsufa don maishe su na zaman.