
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Sifaniya ta doke Argentina da ci 1 da 0 a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na 2026 da aka gudanar a Nahiyar Amurka.
Ɗan wasan Barcelona, Ferran Toress ne ya zura ƙwallon yayin da aka shiga zangon ƙarin mintina 30 bayan kammala 90 ba tare da zura ƙwallo a raga ba.
Wannan shi ne karo na biyu da Sifaniya ke lashe gasar tun bayan ɗauka da ta yi a 2010, a lokacin da aka gudanar da gasar a ƙasar Afirka ta Kudu.
