Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi da ta ‘an jarida tare da wasu ƙungiyoyi a Katsina sun bi sahun masu taya shugaban ƙungiyar ma’aikatan jihar Kwamred Hussaini Hamisu ‘Yanduna samun muƙamin babban sakatare a gwamnatin Katsina.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi reshen Katsina, Kwamred Nasiru Maiwada Maiadua ya bayyana cewa gwamnati ta yi la’akari da kyakkyawan shugabanci da jajircewa wajan kula da jin daɗin ya’yan ƙungiyar NLC a jihar.
Ya bayyana cewa sadaukar da kai da jajircewa wajen cigaban ma’aikatan gwamnatin Katsina ya sanya gwamnatin Dikko Raɗɗa tayi la’akari da wannan gudummuwa da ya bada.
Kwamred Nasiru ya ce wasu daga cikin nasarori da shugaban NLC ya samu sun haɗa da ƙarfafa gwiwar ƙungiyar ƙwadago na ganin an kyautata jin daɗin ma’aikatan jihar.
Haka kuma a lokacin shugabancin ƙungiyar,”gwamnatin Katsina ta aiwatar da sabon tsarin albashi tare da biyan biyan basukan kuɗaɗen fansho da gratuity da ya kai Naira biliyan 42 ga ma’aikatan jihar da suka ajiye aiki a shekarun baya.
Itama ƙungiyar ƙwadago reshen Katsina ta bayyana muƙamin da shugaban ƙungiyar ƙwadago ya samu abinda ya cancanta tare da karfin gwiwar zai yi amfani da ƙwarewar sa na shugabanci wajen cigaban aikin gwamnati a jihar.
Shima tsohon shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta jihar kwamred Mannir Suleiman ya ce wannan muƙami na babban sakatare an aza ƙwarya cikin gurbin ta.
Ya ce babu shakka Gwamna Dikko Raɗɗa bài zaɓen tumun dare ba duba da irin nasarori da ya samu tun yana shugabancin ƙungiyar ma’aikatan lafiya har ya kai ga matsayin shugaban NLC a Jihar.
