
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun tsaro ƙarƙashin Atisayen Haɗin Kai (OPHK) tare da ‘yan sandan MOPOL, sun yi nasarar daƙile wani babban harin garkuwa daga wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne a makarantar Kwalejin Tarayya ta Mata (FGGC) da ke Monguno a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare a ranar Lahadi, 19 ga Yuli a makarantar, wadda a yanzu gwamnatin jihar ke amfani da ita a matsayin wajen kwanan ɗaliban Polytechnic ta Tarayya ta Monguno na wucin-gadi.
Jami’in yaɗa labarai na OPHK, Kyaftin Mohammed Goni ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, inda ya ce maharan sun samu damar zuwa makarantar ne da taimakon wasu abokan hulɗarsu, sannan suka yi yunƙurin sace ɗaliban.
A cewarsa, kasancewar jami’an da ke tsaron yankin sun ankara, an yi musayar wuta tsakaninsu da mayaƙan, wanda hakan ya tilasta wa ‘yan ISWAP ɗin janyewa sakamakon fin ƙarfi da aka nuna musu, yayin da kuma aka tura wasu ƙarin jami’an daga Shiyya ta 3 ta Quick Reaction Force (QRF) a makarantar.
Ya bayyana cewa, ‘yan ta’addar sun tsere ba tare da sun cimma manufarsu ba ta garkuwa da ɗaliban.
Kyaftin Goni ya ƙara da cewa, an samu dameji na wasu sassan makarantar sakamakon musayar wutar, amma an yi nasarar daƙile baki ɗaya farmakin.
Bayan atisayen, dakarun tsaron sun yi nasarar ceto ɗalibai 46, waɗanda tuni aka garzaya da su Barikin Sojoji na Kinnasara a Monguno, inda ake duba lafiyarsu da kuma ba su kulawar da ta dace.
A cewar sojojin, baƙi ɗaya ɗaliban da aka ceto suna nan cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda aka yi garkuwa da shi.
Saidai, Goni ya ce duk da wannan ƙoƙari na dakarun tsaron, an samu wasu ɗalibai da harbin bindigar ‘yan ta’addar ya rutsa da su a yayin ba-takashi da sojojin.
Ya kuma jajenta wa iyalan waɗanda hakan ya shafa tare da tabbatar wa mazauna cewa an ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen ba rayuka da dukiyoyinsu kariya.
