NBTE ta yaba wa Gwamnatin Katsina kan fassara kayan koyon sana’o’i zuwa harshen Hausa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar ilimin fasaha na ƙasa (NBTE) ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina bisa ƙoƙarin ta na fassara kayan koyon sana’o’i zuwa harshen Hausa.

Babban sakataren hukumar ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE), Farfesa Idris Muhammad Bugaje, ya bayyana ƙaddamar da littattafan koyar da sana’o’in fasaha da aka fassara zuwa harshen Hausa a Katsina Youth Craft Village a matsayin wani babban ci gaba da zai sa ilimin sana’o’i ya isa ga al’ummomin karkara cikin sauƙi.

Haka kuma ya yaba wa gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, bisa zuba sama da Naira biliyan biyar wajen bunƙasa cibiyar ta KYCV.

Bugaje ya yi wannan yabon ne yayin wata ziyarar girmamawa da shugabannin Katsina Youth Craft Village suka kai masa a ofishinsa da ke Kaduna, inda suka gabatar masa da sabbin kayan koyarwa da aka fassara zuwa Hausa, domin koyar da sana’o’i daban-daban da cibiyar ke gudanarwa.

A jawabinsa, shugaban NBTE ya ce irin jarin da gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta zuba da kuma jajircewar da ta nuna ya sanya Katsina ta zama ɗaya daga cikin jihohin da suka fi ba da muhimmanci ga bunƙasa koyon sana’o’i a Najeriya.

“Katsina Youth Craft Village na yin aiki mai kyau ƙwarai. Tun bayan zuwan gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa, an ƙara zuba kuɗi da goyon baya sosai, wanda hakan ya ba cibiyar damar cimma waɗannan manyan nasarori.”

Da yake jagorantar tawagar, mai kula da Katsina Youth Craft Village, Injiniya Kabir Abdullahi Ƙofar Soro, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da bai wa koyon sana’o’i fifiko domin ƙarfafa tattalin arzikin matasa.

Ya ce cibiyar na koyar da sana’o’i 14, kuma an samar da littattafan koyarwa tare da fassara su zuwa Hausa domin sauƙaƙa wa al’ummomin karkara fahimtar ilimin fasaha da sana’o’i.

“Mutanen karkara su kan kasance a baya wajen samun ilimin sana’o’i. Amma idan aka fassara waɗannan littattafai zuwa Hausa, ilimin zai fi isa gare su cikin sauƙi.”Inji shugaban.

Ya ƙara da cewa wannan shiri ya samo asali ne daga yadda ƙasashe irin su China suka samu ci gaban fasaha ta hanyar koyar da ilimi cikin harshensu na uwa.

Injiniya Kabir ya bayyana cewa an haɗa gungun farfesoshi da ƙwararrun masana harshe domin tabbatar da ingantacciyar fassarar littattafan, ƙarƙashin jagorancin babban mai ba da shawara, Dakta Shehu Abdulkadir.

Ya kuma bayyana cewa cibiyar na shirin gudanar da bikin yaye ɗalibai karo na biyu a wata mai zuwa, inda ɗalibai 1,662 za su kammala horo a fannoni daban-daban na sana’o’i, adadin da ya ninka kusan sau uku idan aka kwatanta da mutum 600 da aka yaye a baya.

A cewarsa, tsarin bibiyar waɗanda suka kammala horo ya nuna cewa tsakanin kashi 80 zuwa 85 cikin 100 na waɗanda aka horar a baya yanzu suna gudanar da sana’o’i ko kasuwanci da suka danganci ƙwarewar da suka samu.

Tawagar ta kuma bayyana cewa cibiyar na da manajojin tabbatar da inganci na waje (EQAMs) guda uku, manajojin tabbatar da inganci na ciki (IQAMs) guda huɗu zuwa biyar, da kuma sama da masu tantance inganci 100 a shiyyoyin sanatoci na jihar, tare da malamai da masu horaswa kusan 250.

Da yake mayar da martani, Bugaje ya ce yana da tabbacin cewa waɗanda aka horas za su kammala da takardar shaidar ƙwarewar sana’a ta ƙasa (NSQ) ƙarƙashin tsarin ƙwarewar sana’o’i na ƙasa (NSQF). Ya kuma yi alƙawarin halartar bikin yaye ɗaliban.

Ya yaba wa cibiyar kan samar da ingantattun littattafan koyarwa musamman a fannin sana’ar fata, tare da ba gwamnatin jihar shawarar ta yi la’akari da amincewa da amfani da waɗannan littattafai a faɗin ƙasa baki ɗaya.

“Abin farin ciki ne ganin an fassara waɗannan littattafai zuwa Hausa, domin hakan zai sa ɗalibai su fi fahimtar darussa cikin sauƙi. A koyar da sana’a ana iya amfani da kowane harshe na gida.”Inji Bugaje

Ya kuma ba da shawarar a fassara wasu daga cikin littattafan zuwa rubutun Ajami, domin ba almajirai damar koyon sana’o’i, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalar bara.

Ya tuna cewa a zamanin Daular Usmaniyya ta Sakkwato, almajirai na samun tallafin gwamnati tare da koyon sana’o’i a lokaci guda da karatun addini, yana mai kira da a dawo da irin wannan tsari ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin Katsina Youth Craft Village da hukumar makarantun Islamiyya ta jihar Katsina.

Haka kuma ya buƙaci cibiyar ta faɗaɗa yawan sana’o’in da take koyarwa fiye da waɗanda ake da su yanzu, tare da fara horas da ƙwararrun ma’aikata da za su iya aiki a manyan ayyukan raya ƙasa kamar bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), bututun iskar gas na Najeriya zuwa Morocco, da kuma tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla, waɗanda ya ce za su buƙaci dubban ƙwararrun ma’aikata nan gaba.

Bugaje ya yaba wa gwamnatin jihar bisa haɗa shirye-shiryen koyon sana’o’i ƙarƙashin Katsina Youth Craft Village, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa cibiyar za ta ci gaba da samun ci gaba a ƙarƙashin gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa.

Shugaban NBTE, wanda ɗan asalin Jihar Katsina ne, ya ce yana ɗokin halartar bikin yaye ɗaliban domin taya su murnar nasarar da suka samu da kuma ci gaba da gwamnatin jihar ke yi wajen bunƙasa ilimin fasaha da sana’o’i.

By ukarofi

Leave a Reply