Hanyoyin da gwamnati za ta inganta tattalin arziki da magance fatara – Shugaban Bankin Jaiz

Daga UMAR M. GOMBE

ALHAJI HASSAN USMAN shi ne Babban Manajan Darakta na Bankin Musulunci na farko a Nijeriya, wato Bankin Jaiz. A wannan hirar da Mataimakin Editan Manhaja, UMAR MOHAMMED GOMBE ya yi da shi, qwararren masanin tattalin arzikin ya bayyana abubuwa da dama da suka hada da koma-bayan tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta da hanyoyin da za a magance su. Haka kuma ya yi tsokaci kan alfanun bayar da zakka da kuma gudunmawar da bankuna ke bayar wa ta fuskar inganta tattalin arziki, musamman bankunan Musulunci.

MANHAJA: Ran ka ya dade, a matsayin ka na qwararre a bangaren tattalin arziki, me za ka ce kan koma-baya da Nijeriya ta samu kan ta a a halin yanzu ta fuskar tattalin arziki?

Bismillahir Rahmanir Rahim. To wannan hali da muka samu kan mu kamar in ce wani abu ne muqaddari daga Allah, wanda ya shafi duniya gaba daya, wanda ya samo asali daga annobar cutar korona da ta mamaye duniya. Ka san idan aka samu matsala a Chana, to matsalar za ta iya shafar Turai da Amurka har zuwa nan qasashen Afirka gaba daya. Ba Nijeriya ce kadai ta samu komabayan tattalin arziki ba, har da sauran qasashen da tattalin arzikin su ya kai qololuwa a bunqasa. Kamar ita Chana ka ga su kan su a bana sun samu koma baya sosai na tattalin arzikin, ballantana mu nan Nijeriya wanda tattalin arzikin mu ya ta’allaqa ne kacokam a kasuwar mai ta duniya, idan ya yi tsada a kasuwannin duniya, gwamnati za ta samu kudin shiga, tattalin arzikin qasa zai qara tashi, darajar naira za ta qaru.

Saboda haka Nijeriya ta dogara ne da kaso kusan 90 na tattalin arzikin ta ta bangaren man fetur yake fitowa; to kuma ka ga tun daga watan Maris da annobar korona ta bazu aka rurrrufe garuruwa, su kan su jiragen da ke dakon man fetur sai da suka kama yawo a teku babu inda za su je su kai shi. Ka ga waxannan abubuwan su ne suka hadu suka kawo mana cibaya a harkokin tattalin arzikin mu.

Kamar yadda ka ambaci alqaluman da ke nuna cewa wannan koma bayan tattalin arziki ya shafi duniya ne baki daya kuma Nijeriya qasa ce da ke dogaro da man fetur kusan da kashi 90. To me ya kamata gwamnatoci a nan Nijeriya su fi mayar da hankali akai bisa ga wannan darasi duba da cewa akwai harkokin noma, da ma’adinai da sauran su?

Babban abin da gwamnatoci ya kamata su yi shi ne su tabbatar an samu yanayi na kirki wanda zai sa a samu abin dogaro da kai wajen harkar noma da kuma gyara dokokin fannin ma’adinai, amma abu mai sauqi shi ne a inganta harkar noma. Ka san tarihi ya nuna tun kafin a samu ‘yancin kai da noma Nijeriya ta ke tunqaho, irin su noman gyaxa da auduga da masara da kuma irin su kwakwar manja, saboda haka ne ma Turawa suka yi titin jirgin qasa tun daga Legas har Gusau, zuwa Kano, ana daukar gyaxa da auduga da sauran su. To ta haka ake samun kuxin shiga. Ba za a ce akwai wadata kamar yanzu ba, amma ba a samu irin karayar tattalin arziki kamar yadda muke samu yanzu ba, saboda yanayin shugabanci a wancan lokacin. Amma yanzu halin da ake ciki shi ne idan kasuwar mai ta faxi sai tattalin arziki ya fadi. Shi kuma tattalin arziki idan ya yi qasa ya na shafar zamantakewa, yana kuma shafar zaman lafiya da tsaro.

Za a iya cewa yanzu akwai qarancin amana, da cin hanci da rashawa da ke haddasa hakan, idan aka kwatanta da shugabannin baya da ka ke magana?

Wato abin da ke faruwa shi ne, shi kudin mai kamar abun nan ne da Bature ya ke kira Bonanza (bulus). Na farko dai abu ne aka tono a qasa, ko wasu suka tono, wasu mutanen qasa ma ba su san ana tonowa ba, domin ba abu ne da za ka ce a wajen haqar an fasa bututu ko an yi musu varna ko wani abu ba, don haka yawancin mutanen qasa ba su san ana yi ba. Shi mai din ba kamar yadda wasu qasashe su ke yi ba, ya kwarara cikin qasar ne; abin nufi a nan shi ne sun yi masana’antu a qasa ana sarrafa man, sai dai abin da ake nema daga man kamar giris da kwalta ko roba da sauran su. Mu man da muke samu ya na amfanar wasu qasashe ne da ayyukan yi, mu kawai sai dai mu ga kudin, to wannan yana da illa sosai, saboda kamar ba mu wahala ba ne kudin suka shigo, don ha ka abin da ba ka wahala ba kuwa ya fi sauqi ka banzantar da shi akan abin da ka wahala. Don haka ya kamata gwamnatoci su fara nazarin karkata zuwa wasu vangarorin don bunqasa tattalin arziki a maimakon tsayuwa waje guda kamar yadda mu ke gani a halin yanzu.

To a halin yanzu kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta ke daukar matakan rage radadin talauci ga talakawa ta hanyar raba musu tallafi da ake yi ko qananan basuka marasa ruwa, ka na ganin hanya ce mai bullewa kuwa?

To da ana zaman lafiya da bunqasar tattalin arziki, ba abin da gwamnati ya kamata ta yi ba kenan, saboda akwai muhimman abubuwa da su ka fi wadannan, amma tunda an samu durqushewar tattalin arziki gaba daya dole ne gwamnati ta shiga ta tallafa wa jama’a da kudade; saboda idan ba su tallafa din ba wadanda ba su da shi ya za su yi? Za su iya shiga tashin hankali da matsin rayuwa daban-daban. Na biyu, wadanda suke wurare da ma’aikatun sarrafa kayan masarufi za su sarrafa amma babu masu saye, ka ga sai batun rage ma’aikata a cikin su, domin ba za su iya tafiyar da ma’aikatar ba sannan ga albashin ma’aikata, idan kuwa bai rage su ba, to ba za su iya daukar sababbi ba. Wannan wani tarnaqi ne ga tattalin arziki fiye da idan ba a tallafa din ba.

Ran ka ya dade, duba da cewa talaucin ya fi qamari a arewacin Nijeriya ne inda ake kwatanta addinin Musulunci sau-da-qafa, kamar yaya ka ke kallo idan za a yi doka a kan karba da bayar da zakka a Nijeriya don samar da walwala ga jama’a?

Ka san wannan abu ne mawuyaci a qasa irin wannan, wannan zai yi wahala gaskiya. Amma ina tunanin a jihohi za su iya yi daidai gwargwado, musamman jihohin da cikin su akwai wadanda su ka kafa shari’a ta Addinin Musulunci da tafiyar da al’amura bisa tsarin addinin Musulunci, yawancin su za su iya su kawo wannan. To amma ka tuna akwai rashin yarda tsakanin shugabanni da waxanda ake mulka da kuma tsakanin malamai. Saboda haka akwai jihohin da duk da babu doka irin wannan amma suna da ma’aikata ko hukumar da ke kula da tara zakka da rarrabawa ga mabuqata, to amma ba su sa shi a doka ba yadda idan mutum bai bada ba za a je a amsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Domin a tsarin shari’ar Musulunci idan ba ka fitar da zakka ba za a iya bin ka a amsa da qarfin hukuma. To da za a samu yanayi mai kyau wanda za a iya tara zakkar nan, kuma a bi ta yadda addini ya ce, da na san ba za a samu tarin al’ummar da ke da talauci kamar yanzu ba. Saboda idan aka dauka aka ba mutum, zai samu jari, zai fita daga talauci kuma ya dogara da kan sa har ta kai ga wata rana wanda aka ba shi ma ya fitar ya bai wa wani. Sannan kuma za a samu ‘yan uwantaka tsakanin masu hali da marasa hali, mutane za su so junan su; duk wanda ya xauki milyan guda ya damqa maka ya ce wannan zakka ce kai ma ka je ka yi hidimarka, kuma alqawari ne Allah cewa Zai qara wa dukiya albarka, sannan akwai aminci da kariya, domin idan mutane na zuwa gidanka suna karvar zakka, to ka na cikin aminci, duk abin da ya tunkari gidan ka na sharri sai inda qarfin su ya qare, za su tsaya. To alfanu suna da yawa idan ka ci gaba da lissafi.

To idan muka dawo sashen ka na aikace-aikacen banki, ka riqe muqamai a bankuna daban-daban har zuwa yanzu da ka ke Babban Darakta na Bankin Jaiz. Kamar wace rawa bankuna ke takawa wajen farfado da tattalin arziki a Nijeriya?

Ka san shi aikin banki a zamanance ya zama lalura ne dole a same shi saboda zamani ya kai mutane su na cudanya da juna kuma su na wurare mabambanta. Misali, ka na da abokin hulda a Legas ko Kano ko kuma Maiduguri zai iya turo maka kaya kai kuma ka tura masa kudi. Ka ga idan babu banki sai ka dauki kudin ko kayan ka kai masa. Ku ma ya wanzar da cinikayya cikin sauri da kuma hadarin yawo da kudi, da kuma kawar da fargabar kwana da kudi a gida. Ka ga kenan harkokin bankin akwai qaruwa sosai tsakanin masu ajiya da kuma bankunan. Kuma ya na sa tattalin arziki ya bunqasa kuma bankuna su na taimakawa gwamnati ta wajen mu’amalar kudade, domin ita gwamnati ta na lissafin abin da ta ke samu, ba lokaci guda suke zuwa ba, to bankuna suke ba ta kudi kafin daga baya idan kudin su ka shigo a yi balas. Haka nan bankuna su na taimaka wa qungiyoyi da qananan ’yan kasuwa wajen ba su rancen kudi don cigaban kasuwancin su, amma da sharadin idan an nemi kudin nan za su dawo da su.

A qarshe, menene ya bambanta bankin ku na Musulunci da sauran bankuna, saboda a tarihi a baya bankin Jaiz ya yi ta fuskantar qalubale da yawa wanda yanzu kusan za a ce sun zama tarihi. Saboda haka a gurguje kamar menene bambanci tsakanin bankin ku da sauran bankuna?

To babban abin da jama’a su ka fi sani shi ne bankin Musulunci ba ya ta’ammali da riba ko kudin ruwa; banki ne wanda idan ka zo ka ce ka na son a ba ka tallafi ko bashin kudi, to za a tambaye ka me za ka yi da su? Idan abin da za a saya ne a ba ka hayar shi sai a saya a ba ka, a hankali kai ka saye shi daga hannun banki. Idan kuma kudi ne bankin ya na iya ba ka idan ya tabbatar ka cika qa’idoji da sharuddan ba ka bashin, sai ka je ka juya kudin idan ka samu riba ko faduwa sai a raba. Wannan shi ne bambancin mu da sauran bankuna. Ba ma saka kudin ruwa kuma muna daukar asara idan duk an bi hanyoyin tabbatar da hakan. Sannan bankin Musulunci ba sa tu’ammali da mutane ko ’yan kasuwan da qarara an san abin da su ke yi ko kasuwancin su haramun ne ko kuma Musulunci bai yarda da shi ba. Misali, kamar kamfanin giya ya zo ya ce a bude masa asusun ajiya, za mu ce a’a, dukiyar ka ta haramun ce, ba mu so. Sai bambanci na uku; shi Bankin Musulunci akwai kwamitin malamai qwararru wadanda su ka san kasuwanci da harkokin dukiya, duk abubuwan da ake yi a bankin su na sa ido su gani bisa tsarin shari’ar Musulunci. Kuma lokaci zuwa lokaci su na zuwa su duba yadda ake tafiyar da harkokin bankin, idan ma abokin hulda ya na da qorafi zai iya rubuta takarda ko ya taka takanas ya je ya same su ya gabatar da qorafin sa, sai a bi diddigin asalin abin da ya faru don a warware shi ba tare da cutar da kowa ba. To in ban da bankin Musulunci babu mai irin wadannan qa’idojin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *