Qanqara- Tun da Garba ya nemi afuwa

Tare da Nasiru Adamu El-Hikaya

Muhawar yawan xaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina da a ka sace ta zo qarshe tun da an gano yaran ko na ce an samu dukkan yaran har an ma miqa su ga iyayen su. Ba wata baquwar al’ada ba ce a Nijeriya a ba da labari da ya wuce kima ko ya gaza kima musamman hakan ya fi dogara ne ga yadda labarin ya shafi mai ba da shi. Hakanan a lokacin da gwamnati ko jami’an tsaro kan yi qoqarin rage kaifin labari don ta yiwu ya jawo tashin hankali ko zubar da mutuncin hukumomi, waxanda lamarin ya shafa kan so a fitar da gaskiyar labarin kuma ba mamaki ko da akwai qarin gishiri a ciki don duniya ta fahimci irin tashin hankalin da su ke ciki. Koma dai menene, akwai labarun da ba sa buqatar gyaran fuska wajen yaxa su musamman ma misalin wannan labari na sace xaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina, Arewa maso Yammacin Nijeriya.

 In za a tuna a shekarar 2014 an samu irin wannan yanayi lokacin da gwamnatin tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ta yi tababar sace yara mata kimanin 276 a makarantar sakandaren ‘yan mata ta Chibok da ke jihar Borno. Tababar labarin ya sa rashin xaukar matakan da su ka dace wajen ceto matan daga hannun ‘yan Boko Haram har ya kai ga auren wasu daga matan da ‘yan Boko Haram xin su ka yi da ma labarin yiwuwar rasa ran wasu daga cikin su. Hatta wata daga waxanda a ka samu nasarar tattaunawa wajen dawowar su ta zo da jariri wanda ta haifa da ‘yan Boko Haram.

Da wannan dalili ya zama abun nazari in an samu sabuwar gwamnati da ta soki lamirin tsohuwar gwamnati wajen soko-soko da batun matan Chibok ta yi wani abu da zai nuna yara qalilan ne a ka sace daga Qanqara in ma har an dage da cewa an sace su. Zai iya yiwuwa wannan dalili ya sa har a ka shiga yanayi na jita-jita cewa an yi ba ta kashi da varayin koma an gan su daga jirgin sama, kai har ma a ka kai ga batun ai har an ceto su gabanin sahihin lamarin karvo yaran daga yankin jihar Zamfara.

Mai taimkawa shugaban Nijeriya kan labaru Garba Shehu ya nemi gafarar ‘yan Nijeriya don labarin da ya bayar cewa xalibai 10 a ka sace a Katsina amma yanzu ga shi an wayi gari an ga su 344 ban da ma waxanda su ka arce don neman tsira.

Wannan neman afuwa ya zo bayan sadidan ko cul da cul ganin Annabin tsohuwa an ga yara 344 ne a ka karvo daga hannun ‘yan bindiga.

Shehu ya ce ba ya faxi hakan ne tun farko don rage kaifin gaskiyar labarin ko neman shashantar da batun sace yaran ba ne, amma yanayin bayanai ne da ke hannu su ka ambata hakan.

Shehu a shafin sa na Twitter ya ce ya damu da halin da yaran su ka shiga kuma ya na neman afuwar ‘yan Nijeriya don ba da labarin da ya zama ba daidai ba ne.

Garba Shehu ya nanata mubaya’ar sa ga ‘yan Nijeriya da neman a nuna ma sa fahimta kan wannan tuntuven harshe. Da wannan za a iya cewa ko da Garba Shehu da gangan ya ba da labarin farko, to wannan afuwa da ya nema ta na kan hanya kuma za ta rage tunanin jama’a ga cewa jami’an labarun fadar gwamnati ba su damu da tunanin ‘yan Nijeriya ba kan bayanan da su ke furtawa matuqar hakan hanya ce ta tsirar da mutuncin gwamnati.

Wani ma lamarin da ya faru gabanin wannan shi ne bayanin da a ka alaqanta ga Malam Garba Shehu kan yanka manoman shinkafa na Zabarmari, inda ya ce ba su nemi izini ko sanar da jami’an tsaro ba kafin shiga wannan yanki mai hatsari da hakan ya yi sanadiyyar salwantar rayuwar su. Na ga mutane da dama sun nuna vacin rai ainun ga wannan furuci da caccakar Garba Shehu kan hakan har ma wani ya yi addu’ar Allah Ya sanya a kwave shi daga muqamin nasa. Ba inda na ga Garba ya sake komawa kan wannan batu don alamu sun nuna ya shanye dirar mikiya da a ka yi ma sa da kuma xaukar matakan kaucewa faruwar irin hakan, amma kuma da qaddarar ta sake ratsowa sai ya fito fili ya nemi afuwa.