Shugaban Majalisar Dattawa ya taya ‘yan Nijeriya murnar sabuwar shekara

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya taya dukkan ’yan Nijeriya murnan shiga sabuwar shekarar 2021. Yana mai cewa Shekarar 2020 ta zo ma daukacin kasashen duniya cike da kalubale na tattalin arziki, tsaro, lafiya da sauran fannunuka.

“Amma Alhamdulillah duk da haka, wadannan kalubalen ba su karya mana gwiwa na ganin samun kyakykyawar makoma a matsayin mu na mutane da kuma kasa ba. A matsayin mu na majalisar dokoki, mun dade da tsara yadda zamu tunkari abubuwan da shekarar 2020 ta zo da su ta hanyar yin dokokin da za su tabbatar da gudanar da kyakykyawan mulki da cigaban tattalin arziki. Tun kafin zuwan shekarar mun sake fasalin tsarin kashe kudi na shekara-shekara ya koma daga watan Janairu zuwa Disamba kuma muka tabbatar kasafin kudin mu na 2020 ya tafi a kan wannan sabon tsarin. Mun yi wannan canjin ne don inganta harkokin tattalin arziki da bunkasar sa.”

Ya ci gaba cewa, “Barkewar annobar Korona da ta yi sanadiyar rufe tattalin arziki ta yi mummunar illa ga dukkan kasashen duniya kamar yadda ta yi ma hasashe da tsarin tattalin arzikin mu. Daya daga cikin mummunan sakamakon haka ga Nijeriya shine kara fadawa cikin matsin tattalin arziki yan shekaru bayan fitar mu daga na baya.”

“Duk da wannan yanayin, mu na iya godiya ga Allah ganin cewa masifar harkar lafiya da ta matsin tattalin arziki da ta shafi duniya bata yi irin tasirin da kwararru su kayi hasashen za suyi akan Nijeriya ba. Na yi imani cewa wannan ba wai sa’a gare mu ba, amma sai don rashin jinkirin mu na daidaita da sake tsare-tsaren mu su dace da sabon yanayin da muka tsinci kanmu a ciki.”

“Sake bullar annobar ba zai yi mana irin illar da wasu kasashe ke fuskanta ba, matukar gwamnati da mutane ba su yi sakwa-sakwa ba kuma muka dauki darasi daga abubuwan da ke faruwa a wasu wurare.

A don haka muna bukatar shiryawa fiye da lokacin baya don tunkarar 2021 da shekaru wasu zuwa gaba. Dole my tabbatar da mulki na gari ga mutanen mu da samar masu romon dimokaradiyya duk da kalubalen da muke fuskanta.

Majalisar dokoki ta 9 ta tsaya tsaye akan akidar ta na tabbatar da amincewa da kasafin kudi a watan Disamba kafin shigowar shekarar da za’a kashe kudaden, kuma mun yi haka ma a shekarar 2021. Hakanan, mum amince da kudurin dokoki masu yawa da bangaren zartaswa suka gabatar a matsayin dokar kudi don bada goyon bayan mu ga aiwatar da kasafin kudi na 2021 a cikin tsanaki. Mun sha alwashin ganin Nijeriya ta fita daga matsin tattalin arziki a cikin gaggawa a sabuwar shekara.