Abota ita ce auren zamani

Tare da AISHATU GIDADO IDRIS

Zai iya yiwuwa ku kan yi wani tunani irin nawa, na cewar yawancin lokaci idan mutane ba su samu dama ko sa’ar auren wadanda su ke so ba, su kan samu aqalla wadanda su su ka fi alheri a gare su. Haka abin yake! Domin sau da yawa wasu su kan yi qorafin cewa rayuwa ta juya masu baya idan su ka rasa abin da su ka fi da so.

Ba haka ba ne kuma. Tabbas, ana yawan auren soyayya, amma kuma ana yawan aure na sa’a, dace ko auren sakamako a kan rasa wani ko wata da mutum ke so. Amma kuma wani hanzari ba gudu ba, wasu su kan dauka soyayya ce kawai ta ke tafiyar da aure, wanda ba hakan ba ne kamar yadda mu ka gane daga baya-bayan nan da ilimi ya qara nisa.

Yanzu mun san akwai ‘abota’ da ke biyo bayan ‘daciya’ – watau dacewa da juna – da masoya su ke ganewa da kan su, saboda sai ka ga su na son abubuwa da yanayi iri daya.Wannan kuma ya na daya daga cikin abubuwan da zamani ya yi na’am da su. Misali, wannan na son fim din Indiya, wannan ma na so; wannan na son shinkafa da wake, wannan na son alala, sai sayen wake ya zama alheri a wannan gida. Kuma a yi ta dinar wake!

Idan kowa na son wasan Hausa kuma shi kenan. Idan dukkan su mata da miji su na so, sai su sha kallon su, su na yi su na daukar darasi. Kun ga an dace! Ya kuma ku ka gani idan wannan na son mutane, wancan na son jama’a? Ana tare, inji ‘yan zamani!To kun gani da wuya su yi fada. Sha’awar abubuwa iri daya shi zai qara sa su zama daya. Inda yanayi ya zama daya, ai akwai zaman lafiya kenan.

Wasu kuma, idan masu son labarai ne na duniya, da wuya su yi fada, sai dai su yi ta qosawa wanin su ya samu dama a yi ta tattaunawa. Kuma ko sun yi musu, wannan ba komai, shi ma ana tare. Babu abin da ya fi tashin hankali a wannan rayuwa da ya wuce cewar akwai so da qauna, amma babu abota saboda rashin dacewa wajen abubuwan da mata da miji su ke so ko ba su so.

Amma fa hakan ba shi zai sa zaman lafiya ya yi qaranci ba idan dai kowa zai riqe ra’ayin shi. Domin ko masu bambancin ra’ayin su na zaman lumana idan dai su na da fahimtar juna.Akwai lokacin da na kan ji ana cewa ai bambancin ya kan sa wasu su ga kamar su ba su burge junan su. A kan yi irin wannan harsashen shi ma.

To ba fa a nan take ba, tunda abu daya ke gyara zamantakewa ko ya vata. Wannan abu shi ne fahimta. Idan babu fahimta, ba dole ne a zama daya ba, shi kenan. Amma babu kyau cewar ga bambancin ra’ayi, ga rashin fahimta, sai ka ga ko wani dogon labari ko wata tattaunawa mai tasiri babu tsakanin matar da mijin. Hakan babu dadi. Sai idan babu mutane kusa, kuma zama ya yi zama, sun hadu a daki su biyu, sai ku ga ba wata magana mai tsawo. Kowa ya yi shiru. Ina amfani?

Maimakon idan har mace da namiji su na tare su cika da bayanai da tattaunawa yadda ya kamata domin kuwa ta wannan hanyar ne ake iya qara fahimtar juna, kuma su qara wa juna ilimi tare da shaquwa. Amma ina! Sai dai kowa ya dauko waya don neman abokin hira? Ai ka yi hira don ka na son hira da wasu, amma kada ka so ka rinqa hira don ka rasa abokin hira a abokin zaman ka. Hatsari ne!

Abin da na ke son fadi a nan shi ne gara ku sa mazajen ku ko matan ku a jerin abokan ku na zaman duniya domin ya na rage wasu laifuka da a kan yi wa juna a wannan zamanin. A duba a gani. Tabbas, wannan duniya mun zo mu’amula ne da juna, ba mun zo mu’amula ne da na’ura ba. Saboda haka qoqarin gabatar da kyakkyawar mu’amula shi ya kamata ya zama a gaban mu. Amma tun da farko rashin zama abokan juna ya na sa ma’aurata su zama baqin juna a yawancin lokaci. Kuma abota ita ce sitiyarin tuqin motar auratayya a ko’ina a duniya, da kuma samun dacewa daga Allah.

ReplyForward

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *