Kotu ta garqame asusun bankunan dan majalisa a Kaduna

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna

Babar Kotun Jihar Kaduna ta ba da umurnin a garqame asusun ajiyar bankuna har guda 14 na dan majalisar jiha mai wakiltar Doka da Gabasawa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar, Honarabul Haruna Inuwa Dogo Mabo.

Kotun ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne a bisa samun sa da laifin cin amana da zamba cikin aminci da kuma sama da fadi da kunnen qashi da ya nuna wajen qin biyan dimbin basussuka na kudaden da ya amsa a hannun jama’a da sunan bashi.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin sakatariyar lauya mai gabatar da qara, Zainab Isiaka a wani kwafin takardar da kotun ta tura wa daukacin bankuna 14 wadanda Hon. Mabo ke amfani da su.
Babbar kotun ta baiwa dukkan bankunan umurnin cewa daga yanzu su riqe duk wasu kudade da suka shigo asusun ajiyar dan majalisar domin yin amfani da kudaden wajen biyan dimbin basukan al’umma da suke bin sa har zuwa lokacin da adadin kudaden suka isa a biyan jama’a haqqoqin su, sannan a sakar masa ragamar asusun ajiyar tasa.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*