Wani jami’in Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ya rasa ransa a yayin da yake ƙoƙarin kama wani dillalin miyagun ƙwayoyi da ya tsere bayan an kama shi.
Jami’in ya rasu ne bayan da ya nutse a kogin Ethiope a yayin da yake bin wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a garin Obiaruku da ke ƙaramar Hukumar Ukwuani ta Jihar Delta a ƙarshen mako.
Shaidu sun ce jami’an NDLEA da ke yankin sun kama wani wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, a yayin da yake safarar haramtattun ƙwayoyi, sannan suka nufi wurin gadar kogin Ethiope domin kai shi ofishinsu.
Majiyoyi sun ce ba zato ba tsammani wanda ake zargin ya kuɓuce daga hannun jami’an, inda ya tsunduma cikin kogin domin tserewa.
Wata majiya ta ce wasu jami’an NDLEA sun shiga cikin kogin da nufin sake kama shi, amma aka yi rashin sa’a, ɗaya daga cikinsu ya nutse.
An yi nasarar ceto wani jami’in da ya shiga kogin tare da shi, aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likita.
Shi kuwa wanda ake zargin ya samu damar tserewa ta cikin kogin.
Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ta bayyana abin da ya faru a matsayin abin mamaki, tana mai cewa zurfin kogin bai kai yadda mutum zai nutse a cikinsa ba.
Ta ce, daga bisani an gano gawar jami’in, sannan aka miƙa ta ga NDLEA bayan da al’ummar Obiaruku suka gudanar da wasu al’adun gargajiya da ake yi a irin wannan yanayi ga mutanen da suka nutse a kogin Ethiope.
Da aka tuntuɓi Kwamandan NDLEA na Jihar Delta, Halilu Hamidi, ya mayar da manema labarai ga kakakin hukumar na ƙasa, Femi Babafemi, domin samun bayani.
Sai dai wani jami’in NDLEA ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya jawo mutuwar jami’in da kuma sauran abubuwan da suka shafi lamarin.
