Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Hukumar da ke kula da asibitoci da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta Jihar Nasarawa (NASPHFIRA), ta taya Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya, Dr. Ibrahim Adamu Alhassan murna a ranar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ta yaba da jajircewarsa da sadaukar da kai wajen cigaban jihar, musamman a fannin lafiya.
Yabon ya zo ne a cikin saƙon taya murna da babbar sakataren hukumar, Dr. Nana Awaya Emeribe, ta aiko a madadin shugabanci da ma’aikatan hukumar.
Suma da suke zantawa da wakilinmu a yayin bikin ranar haihuwar babban sakataren a Lafia, wasu masu ruwa da tsaki da ‘yan ƙasa sun bayyana Dr. Alhassan a matsayin gogaggen mai gudanarwa da jajirtaccen ma’aikacin gwamnati kuma ginshiƙi a fannin lafiya a Jihar Nasarawa.
Sun ce ba shakka jajircewarsa da tawali’unsa da gogewarsa mai yawa na cigaba da bada gagarumar gudummawa ga sauye-sauye da cigaban tsarin kiwon lafiya a jihar.
Wadanda aka zanta da su sun kuma yaba da kyakkyawar mu’amalarsa da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar lafiya ciki har da NASPHFIRA inda suka ce manufofinsa na buɗe ƙofa da jagorancinsa sun ƙarfafa haɗin kai da inganci wajen bayar da hidimar lafiya.
“A madadin hukumar da al’ummar Jihar Nasarawa baki ɗaya muna addu’ar Allah ya ba shi lafiya da ƙarin hikima da shekaru masu yawa na hidima mai amfani ga Jihar Nasarawa da bil’adama baki ɗaya.
“Muna kuma roƙon Allah maɗaukakin sarki ya cigaba da ba shi lafiya da hikima domin cigaba da bada gagaruman gudummawa kamar yadda yake yi a yanzu wajen inganta hidimar kiwon lafiya da kuma cigaban jiha da ƙasa baki ɗaya,” in ji su.
