Shugaban hukumar gudanarwa na hukumar alhazai a Katsina ya ajiye muƙamin sa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar gudanarwa na hukumar alhazai a Jihar Katsina Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai ya ajiye muƙamin sa.

A wata takarda da ya sanyawa hannu kuma ya aikewa sakataran gwamnatin Jihar Katsina,duk da cewa babu wani bayani game da wannan mataki da ya ɗauka,Alhaji Bature ya nuna godiyarsa ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya bashi damar hidimtawa jihar.

Tsohon shugaban hukumar alhazai ya bayyana cewa zamansa a hukumar ya bashi damar sadaukar da kansa wajen bautawa jihar sa da yace haka ma yana miƙa godiya ga gwamnatin Jihar Katsina.

Sarkin Alhazai ya kuma bayyana jin daɗin sa da haɗin kai da goyon bayan da ya samu a wajen sakataran gwamnatin Jihar, majalisar zartarwa ta jiha, ma’aikatan hukumar alhazai da sauran masu ruwa da tsaki bisa iron goyon baya da aka bashi a lokacin da yake riƙe da muƙamin.

Mutum na uku masu riƙe da muƙamin siyasa a gwamnatin Dikko Raɗɗa suka ajiye muƙamin su a ‘yan kwanakin nan.

By ukarofi

Leave a Reply