Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin samar da aƙalla kashi 70 cikin 100 na muhimman kayayyakin kiwon lafiya a cikin gida nan da shekarar 2030, a wani mataki na ƙarfafa wadatar magunguna da rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Iziaƙ Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas, yayin da yake buɗe bikin baje kolin masana’antun magunguna na Nijeriya karo na takwas, wanda ƙungiyar Masu Harhaɗa Magunguna ta ƙungiyar Masana’antun Nijeriya (PMG-MAN) ta shirya.
Taken taron shi ne “Bunƙasa Masana’antu a Yankin Afirka: ƙarfafa Ikon Afirka kan Masana’antar Magunguna da Kimiyyar Rayuwa ta Hanyar Samar da Kayayyaki a Cikin Gida”.
Taron ya haɗa masu ruwa da tsaki daga sassan masana’antar magunguna da kimiyyar rayuwa ta Nijeriya domin tattauna hanyoyin bunƙasa samar da magunguna a cikin gida da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Salako ya ce Shirin Shugaban ƙasa na Buɗe ƙofofin Sarkar Darajar Harkokin Kiwon Lafiya (Presidential Initiative to Unlock the Healthcare Value Chain – PVAC) ya samu alƙawuran tallafin kuɗi da suka kai kusan Dala biliyan biyu, a kan riba mai ƙaranci, inda kusan kamfanonin kiwon lafiya 50 na Nijeriya ke kan matakin ƙarshe na tattaunawa domin samun tallafin. Ya ce Gwamnatin Tarayya na kuma amfani da matakan haraji da wasu manufofin kuɗaɗe domin tallafa wa masana’antun magunguna na cikin gida.
A cewarsa, masana’antun cikin gida 87 na cin gajiyar umarnin shugaban ƙasa da ya tanadi cire harajin kwastom gaba ɗaya kan injinan kera magunguna, sinadaran da ake amfani da su wajen samar da magunguna (APIs) da sauran sinadaran haɗa magunguna, a ƙarƙashin kusan lambobin kayayyaki 1,000 na tsarin rarrabe kayayyakin ciniki na duniya.
Ya ce matakan na da nufin ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma samar da ingantacciyar kariya ga tsarin samar da kayayyakin kiwon lafiya na Nijeriya daga tangal-tangal.
Da yake ƙara bayani, Salako ya ce matsalolin da aka fuskanta a lokacin annobar COVID-19 sun bayyana haɗarin da ke tattare da dogaro da tsarin samar da kayayyaki na duniya. Ya ce, lamarin ya kuma ƙara nuna muhimmancin da ke tattare da bai wa Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka damar gina ƙarfin masana’antun cikin gida domin samar da magunguna, alluran rigakafi, kayan gano cututtuka da sauran muhimman fasahohin kiwon lafiya.
“Maganar da muke yi a yanzu ba za ta ƙara tsaya wa kan ko za mu iya samun magunguna ne kawai a lokacin da tsarin samar da kayayyaki na duniya ke aiki yadda ya kamata ba,” inji shi.
Salako ya bayyana wadatar magunguna a matsayin wani muhimmin al’amari da ya shafi juriyar ƙasa da ikon mallakar kanta, yana mai cewa Nijeriya na buƙatar gina ƙarfin masana’anta a dukkan sassan sarkar darajar magunguna, maimakon mayar da hankali kawai kan haɗa magungunan da aka riga aka samar a ƙasashen waje.
Ya ce shirye-shiryen da gwamnati ke ci gaba da aiwatarwa sun haɗa da faɗaɗa samar da sinadaran da ake amfani da su wajen ƙera magunguna, alluran rigakafi, magungunan ƙwayoyin halitta, kayan gano cututtuka da sauran kayayyakin kiwon lafiya a cikin gida.
Ministan ya kuma ambaci fara aiki da Cibiyar ƙarfafa ƙwarewa da Samar da Samfuran APIs ta Cibiyar Nazarin Magunguna da Bunƙasa Su ta ƙasa (NIPRD), da kuma ƙoƙarin samar da manyan masana’antun APIs na kasuwanci. Ya ce gwamnati na kuma ƙoƙarin samar da kayan gano cututtukan HIV, hepatitis da syphilis a cikin gida, maimakon ci gaba da dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.
Bugu da ƙari, Salako ya ce Nijeriya na buƙatar ƙara zuba jari a bincike da bunƙasa fasahohi, tare da amfani da albarkatun tsirran magunguna da ƙasar ke da su domin zurfafa masana’antar magunguna.
Salako ya ce kafa Medipool, wato ƙungiyar Sayen Magunguna da Kayayyakin Kiwon Lafiya ta ƙasa, za ta taimaka wajen samar da tabbatacciyar kasuwa ga kayayyakin da masana’antun cikin gida ke samarwa. Ya ce ƙungiyar za ta haɗa buƙatun sayen magunguna da kayayyakin kiwon lafiya, ta tattauna farashin sayen kayayyaki masu yawa, tare da inganta tsarin samar da kayayyaki da rarraba su.
Ministan ya kuma yi kira ga masu harhaɗa magunguna, masu bincike, masu zuba jari da abokan hulɗar ci gaba da su duba damar da kasuwannin yankin Afirka ke bayarwa a ƙarƙashin yarjejeniyar ƙungiyar Ciniki Mai ‘Yanci ta Nahiyar Afirka (AfCFTA).
Ya ce cimma burin Nijeriya na bunƙasa masana’antar magunguna zai dogara ne kan ci gaba da zuba jari, ƙirƙire-ƙirƙire, daidaita dokokin gudanar da harkokin masana’antu da kuma samun damar shiga manyan kasuwannin yankin.
