Biyan bashin cikin gida ya ragu zuwa tiriliyan N2.14 a tsakiyar 2026 – DMO

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Biyan kuɗaɗen bashin cikin gida da Nijeriya ke bi ya ragu da kusan Naira tiriliyan ɗaya a tsakiyar shekarar 2026, inda ya koma Naira tiriliyan 2.14 daga Naira tiriliyan 3.14 da aka biya a farkon shekarar.

Bayanan Hukumar Kula da Bashin ƙasa (DMO) sun nuna cewa raguwar ta kai kashi 31.8 cikin 100 idan aka kwatanta da lokutab baya, duk da cewa jimillar bashin gwamnati ta ƙaru a cikin wannan lokaci.

Bayanan DMO sun nuna cewa kuɗaɗen ruwa da na haya sun kai Naira tiriliyan 1.98 daga cikin jimillar kuɗin hidimar bashin da aka biya a zango na biyu, yayin da biyan asalin bashin ya tsaya a Naira biliyan 164.28.

Takardun Bashin Gwamnatin Tarayya (FGN Bonds) ne suka lashe mafi yawan kuɗaɗen hidimar bashin cikin gida, inda kuɗaɗen ruwa da aka biya a kansu suka kai Naira tiriliyan 1.39 a cikin zangon.

Gwamnatin Tarayya ta biya Naira biliyan 530.84 a matsayin kuɗin ruwa na FGN Bonds a watan Afrilu, Naira biliyan 332.49 a watan Mayu, da Naira biliyan 525.05 a watan Yuni.

Haka kuma, kuɗin ruwa da aka biya kan Takardun Baitulmalin Nijeriya (Nigerian Treasury Bills – NTBs) ya kai Naira biliyan 488.80. Daga cikin wannan adadi, an biya Naira biliyan 180.64 a watan Afrilu, Naira biliyan 201 a watan Mayu da Naira biliyan 107.16 a watan Yuni.

Kuɗaɗen haya da aka biya kan takardun bashin Musulunci na Gwamnatin Tarayya (FGN Sukuk) sun kai Naira biliyan 92.29.

Haka kuma, kuɗaɗen ruwa kan Takardun Ajiyar Kuɗi na Gwamnatin Tarayya (FGN Savings Bonds) sun kai Naira biliyan 4.66, yayin da na Takardar Bashin Gwamnatin Tarayya ta Koren Tattalin Arziki (FGN Green Bond) suka kai Naira biliyan 5.56.

Waɗannan alƙaluma sun ƙara nuna yadda biyan kuɗaɗen ruwa ke ci gaba da ɗaukar mafi girman kaso na kuɗaɗen da Nijeriya ke kashewa wajen hidimar bashin cikin gida.

By ukarofi

Leave a Reply