Daga AISHA ASAS
Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Taurari na jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja, shafin da ke kawo muku labaran fitattun jarumai da abubuwan da suka shafi harkar nishaɗantarwa, tare da waiwayar rayuwarsu da abubuwan da suka taimaka wajen kai su inda suke a yau.
A wannan makon, shafin Taurari ya lalubo muku labarin Fiona Fullerton, jarumar da aka haifa a Ungwan Sarki da ke Kaduna, wadda tun tana yarinya ta fara taka rawa a fina-finai, kafin daga bisani ta shiga duniyar James Bond. Amma bayan shaharar da ta samu a matsayin Bond Girl, akwai wani labari mai ban sha’awa na rayuwa, sauye-sauye da sabbin hanyoyin da ta bi bayan ta bar duniyar fim.
Akwai wasu mutane da aka haifa a wani wuri, amma labarin rayuwarsu ya wuce iyakar wurin da aka haife su. Akwai kuma waɗanda idan aka ambaci sunansu, sai a tuna da wata ƙasa, wani birni ko wani tarihi da suka taɓa shiga.
Irin wannan ne labarin Fiona Elizabeth Fullerton, wadda aka haifa a Ungwan Sarki da ke Kaduna a ranar 10 ga Oktoba, 1956. Daga wannan unguwa ce rayuwarta ta fara tafiya har ta kai ta duniyar fina-finai, talabijin da gidan wasan kwaikwayo na Birtaniya, kafin daga bisani ta shiga ɗaya daga cikin fitattun fina-finai na duniya, wato James Bond.
A yau, idan aka ambaci Fiona Fullerton, mutane da dama za su fi tunawa da ita a matsayin Pola Ivanova, matar da ta fito a fim ɗin ‘A View to a Kill’ tare da Roger Moore, wanda ya taka rawar James Bond. Amma kafin a san ta da wannan suna, akwai wata yarinya da ta fara hawa matakan shahara tun tana ƙarama. Tun kafin ta san cewa wata rana za a kira ta da Bond Girl, ta fara da zama Alice a ɗaya daga cikin fitattun labaran yara da aka mayar fim. Kuma kamar yadda labarinta zai nuna, Alice da Pola Ivanova ba su ne ƙarshen tafiyar wannan yarinya ba.
Shin wace ce Fiona Fullerton?
Fiona ita ce kaɗai ’yar Bernard da Pamela Fullerton. Ko da yake an haife ta a Kaduna, ƙuruciyarta ba ta kasance a wuri guda ba. A lokacin da take girma, ta zauna tare da iyayenta a wurare daban-daban da suka haɗa da Singapore, Jamus da Amurka, kafin daga baya rayuwarta ta koma Birtaniya, inda aka fara gina tushen sana’ar da za ta sa sunanta ya wuce iyakar inda aka haife ta.
Tun tana yarinya, burinta shi ne ta zama ’yar rawa. Ballet ce ta fara jan hankalinta, har aka tura ta makarantar Elmhurst Ballet School da ke Surrey domin samun horo. A nan ne labarinta ya fara ɗaukar wata sabuwar hanya, domin abin da ta shiga makaranta domin ta koya a matsayin rawa shi ne daga baya ya taimaka wajen kai ta wata sana’a dabam, wato wasan kwaikwayo. Wataƙila a lokacin ba ta san cewa wannan mataki na ƙuruciyarta zai zama farkon tafiya mai tsawo ba, amma a hankali ƙofofi suka fara buɗewa a gabanta.
Wannan yana daga cikin abubuwan da suke sa labarin rayuwarta ya zama na musamman. Ba wai kawai ta samu damar shiga fim ba ne; ta shiga wannan duniyar tun tana yarinya, kafin ma ta samu damar sanin irin girman hanyar da ta fara bi. Kuma a cikin wannan tafiya, ta samu rawar da za ta sa masu kallon fina-finai su fara gane ta.
A shekarar 1969, lokacin da take kusan shekara goma sha biyu, ta fara fitowa a fim ɗin ‘Run Wild’, ‘Run Free’. Bayan shekaru biyu, ta sake bayyana a Nicholas and Alexandra, inda ta taka rawar Grand Duchess Anastasia. Sai a shekarar 1972 aka ba ta rawar da za ta fi sanya sunanta a zukatan masu kallon fina-finai tun daga ƙuruciyarta, wato Alice.
Yaushe ’yar Kaduna ta zama Alice?
A lokacin da Fiona ta taka rawar Alice a ‘Alice’s Adventures in Wonderland’, tana da shekara goma sha biyar ne kawai. Wannan ba ƙaramin matsayi ba ne ga yarinya da har yanzu take cikin shekarun ƙuruciya, musamman idan aka tuna cewa fim ɗin ya buƙaci ta kasance a tsakiyar labarin da wasu manyan jarumai suka kewaye.
Saidai wannan rawar ta zama babbar kafa a rayuwarta. Daga nan ne Fiona ta fara bayyana ba kawai a matsayin yarinyar da aka gano tana da baiwar rawa ba, har a matsayin ’yar wasan kwaikwayo da za a iya ɗora wa manyan rawuna. Alice ta zama ɗaya daga cikin rawar da za a riƙa danganta ta da ita, duk da cewa a lokacin ba ta san irin yadda wannan suna zai ci gaba da bin ta ba.
Bayan Alice, talabijin ma ta buɗe mata wata ƙofa. A shekarar 1975 ta kasance cikin jaruman farko na shirin BBC mai suna ‘Angels’, sannan ta ci gaba da fitowa a wasu shirye-shirye da suka haɗa da ‘The Charmer’, ‘Hold the Dream’ da ‘Shaka Zulu’.
A wannan lokacin, rayuwar Fiona ta riga ta fara nuna mata cewa sana’ar wasan kwaikwayo ba hanya ce guda ɗaya ba. Wasu lokuta kyamara ce ke buɗe ƙofa, wani lokaci kuma dandalin wasan kwaikwayo ne. Kuma duk lokacin da ta shiga wata sabuwar hanya, sai ta ƙara samun damar nuna wani ɓangare na baiwarta da ba a taɓa gani ba.
Daga kyamara zuwa dandalin wasan kwaikwayo:
A shekarar 1982, Fiona ta samu wata muhimmiyar dama a West End na London, inda ta taka rawar Guinevere a wasan Camelot tare da fitaccen ɗan wasan kwaikwayo Richard Harris. Wannan ba kawai wani ƙarin aiki ba ne a cikin jerin ayyukanta; mataki ne da ya nuna cewa iyawarta ba ta taƙaita da fitowa a fim ko talabijin ba. Ta iya tsayawa a dandalin wasan kwaikwayo, ta ɗauki rawa a gaban masu kallo, tare da haɗa baiwar wasan kwaikwayo da ƙwarewar da ta fara samu tun tana yarinya.
Sunan Fiona yana cikin kundin Camelot na London na shekarar 1982 tare da Richard Harris, kuma muryarta tana cikin waƙoƙin wasan da aka adana daga wannan shirin. Daga baya ta sake taka rawar Eliza Doolittle a Pygmalion a Chichester Festival Theatre, abin da ya ƙara nuna yadda ta ci gaba da samun matsayi a gidan wasan kwaikwayo.
Sai dai duk da waɗannan rawar, wato daga Alice zuwa Guinevere, ba su kai ga abin da zai zama ɗaya daga cikin abubuwan da aka fi danganta sunanta da shi ba.
A shekarar 1985 ne labarin ya sauya fuska, lokacin da ta samu damar shiga wani fage da ya riga ta yi suna a duniya.
Yadda Fiona ta shiga duniyar James Bond:
Lokacin da aka fara shirin A View to a Kill, fim ɗin James Bond na shekarar 1985, Fiona ta samu rawar Pola Ivanova, wata jami’ar KGB. Ta fito tare da Roger Moore, wanda a lokacin shi ne James Bond.
Daga nan ne sunanta ya shiga wani sabon rukuni na tarihi, wato matan da suka taɓa fitowa a cikin duniyar James Bond. Ga yarinyar da ta fara tafiyarta a Kaduna, wannan wani sabon mataki ne na shahara, domin yanzu ta shiga cikin wani fim da sunansa ya riga ya zama sananne ga masu kallon fina-finai a sassa daban-daban na duniya.
Lokacin da rayuwa ta fara canza mata hanya:
A shekarun da suka biyo bayan shahararta, Fiona ta ci gaba da aiki a fina-finai da talabijin, amma a hankali rayuwarta ta fara karkata zuwa wani wuri dabam.
Ta yi aure da ɗan wasan kwaikwayo Simon MacCorkindale a shekarar 1976, inda auren ya kai ƙarshe a shekarar 1981. Bayan wasu shekaru, ta sake yin aure da Neil Shackell a shekarar 1994. Wanda auren ya yi albarka da samun ƙaruwa ta ‘ya mace mai suna Lucy, wadda aka haifa a shekarar 1895. Wannan kuwa ya ƙara ɗora ƙarin nauyi ga jarumar wato na zama uwa.
Saidai a shekarar 1996 wani abin da ya faru a gidanta ya ƙara canza yadda take kallon rayuwar shahara. A lokacin tana gidanta dake Weybridge, Surrey, tana kula da ’yarta Lucy wadda take da watanni biyar. Wani mutum ya zo ƙofarta, saidai abinda ya faru ya kasance na tashin hankali gare ta duk da cewa shahara ce sanadi.
A wannan lokacin, Fiona ta fara ja da baya daga hasken da ta shafe shekaru a cikinsa. Amma ja da baya daga fim ba yana nufin ta daina neman abin da za ta yi da baiwarta ba. A maimakon haka, wani sabon shafi ne ya buɗe a rayuwarta, wanda ba lallai ne masu kallon fina-finai su yi hasashen za ta shiga ba.
Bayan ta koma rayuwa mai nisa da hayaniyar masana’antar fim, Fiona ta fara shiga harkar kadarori. Da farko ta fara saye, gyara da kuma kasuwancin gidaje, musamman a London da Surrey. Abin da ya fara a matsayin wani sabon fanni na rayuwarta ya girma har ya zama sana’ar da ta dogara da ita. Bayan wannan ta kuma fara rubuce-rubuce da ba da shawarwari kan harkar kadarori.
A shekarar 2001, The Irish Times ta rubuta cewa tana gudanar da harkar saye, gyarawa da bayar da gidaje haya, tare da rubuce-rubuce kan harkar kadarori. A wannan lokacin ta wallafa littafinta ‘How to Make Money From Your Property’. Daga nan ne wata sabuwar baiwa ta fito, wato rubutu da koyar da abin da ta koya daga aikinta.
Ta rubuta littattafai uku da suka shafi kadarori: ‘How to Make Money From Your Property’ a shekarar 2001, ‘Fiona Fullerton’s Guide to Buying, Selling & Moving House’ a shekarar 2003, da ‘Fiona Fullerton’s Guide to Buying to Let’ a shekarar 2004.
Za mu ci gaba.
