
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya bayyana ƙwarin-gwiwarsa ta cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen 2027 a jihar Kogi da gagarumar nasara.
Rahotanni sun nuna cewa Yahaya Bello, wanda shi ne ɗan takarar sanatan Kogi ta Tsakiya a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, ya kuma bayyana ƙwarin-gwiwar cigaba da samun goyon al’ummar gundumar ga APC da jagorancinta. Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi taron magoya bayan APC yayin da ya kai ziyara a Kogi ta Tsakiya.
“Ban taɓa kokwanton mutanena suna tare da ni ba ɗari bisa ɗari. Ban taɓa kokwanton cewa mutanena suna goyon bayan APC ba ɗari bisa ɗari,” inji Yahaya Bello. Ya bayyana tarbar da suka masa a matsayin nuna ƙarfin alaƙar da ke tsakaninsa da ‘yan jihar, waɗanda ya yi wa gwamna daga shekarar 2016 zuwa 2024.
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana ƙwarin-gwiwa kan samun goyon bayan ‘yan Kogi ga Tinubu da Gwamna Ahmed Ododo, yana mai cewa al’ummar sun fahimci alƙiblar gwamnatin APC a matakin tarayya da jiha.
Kazalika, ya yi godiya ga Ubangiji, APC, Tinubu, Ododo da kuma mambobin jam’iyyar APC a baki ɗaya matakai bisa goyon bayansu, yana mai bayyana taron a matsayin tsarin jam’iyyar daga tushe a jihar.
