Raud al-jinan: Gudunmawar Waziri Gidado bin Laima

Tare da FATUHU MUSTAPHA

Kwanakin baya, Farfesa Malumfashi Ibrahim ya janyo hankalina a wani rubutu da wani masani daga Kasar Amurka: Hui Xinpeng ya yi a kan shahararren littafin nan da Wazirin Sokoto : Gidado bin Laima ya rubuta a kan karamomim Shehu Usman bin Fodio, wannan rubutu ya burgeni, kuma har na kwafa na sanya shi a bango na na Facebook. To Amma ba wannan ne ya dauki hankali na ba, wani abu ne ya faru wasu mutum biyu daga cikin mutanen da suka yi koment a kan bayanin, sun kira littafin da tatsuniya: wannan abu ya bani mamaki Matuka!

Na farko dai na tabbatar ba su san waye sheikh Gidado bin Laima ba. Na biyu, na tabbatar da ba su karanta shi littafin na Raudul Jinan ba. Hakan ta sanya na ga, a maganar gaskiya ba su yi wa marubucin littafin adalci ba (ina da PDF copy na littafin). Wannan ce ta sanya na yi wannan rubutu a kan wannan babban malami kuma basarake a Daular Usmaniyya.

Ya kamata a sani bani na fara rubutu a kan Raudul Jinan ba, wannan littafi ya shahara da har manyan jami’o’i na duniya da ake kira da, Ivy league wadanda ake ji da su a duniya, irin su Princeton da Havard suna nazartar wannan littafi domin fahimtar matsayin karamar waliyai a wurin sufaye. An wallafa kundayen digirin digirgir har guda biyu a Princeton a kan wannan littafi. Farfesa Murray Last ya gabatar da kasida a JSOAS a kan wannan littafi, Farfesa Philip Shea ya yi bayani a kan wannan littafi, R O Adeleye (marubucin littafin Power and Diplomacy in Sokoto caliphate) ya gabatar da kasida a kan wannan littafi, Neil Skinner ya yi tsokaci mai zurfi a kan ta. Anya kuwa duk wadannan sa bata lokacin su a kan tatsuniya? Kai kari wallahi ma kacokan Mervyn Hisket ya daura fahimtar sa (theory) din sa na fahimtar “karama” da Mu’ujiza a kan wannan littafi.

Wannan marubuci ya wallafa litattafai, cikin su kuwa har da: Majma’u wanda ya yi bayani a kan su waye almajiran Shehu, al Kashf wal bayan a kan su waye ahlin Shehu, sai kuma Raudul Jinan a kan karamomim Shehu Usman. An shaida da cewa waziri Gidado gogaggen malami ne, masani, arifi, kuma mutafannini. Ya kuma kware a sha’anin mulki, domin ya taka rawa a alamuran siyasar daular Sakkwato a zamanin da yake waziri.

An haifi malam Gidado a shekarar 1776 a birnin Konni dake Kasar Niger a yau. Nisabar sa ita ce “Gixaxo sunansa na gaskiya Uthman (Gidado) b. Abu Bakr (Sambo Laima) b. Umar (Gabinda) b. Ahmad. Ya zauna tare da mahaifin sa a wurin Shehu tun ana Degel. A zamanin jihadi, bai jagoranci wata runduna ta Kabilar Fulani ba, amma dai dan asalin Kabilar Torobbe ne. Shi aka daurawa alhakin tattara gudunmowar kudaden da aka yi jihadi da su. Wannan dama ce ta sanya ya san kusan dukkan manyan Kabilun Fulani da suka yi jihadi.

Tun bayan rasuwar Shehu Usman ne, rashin fahimta ta taso, tsakanin Shehu Abdullahi (Abdullahi Gwandu, ko Abdullahi mai Bodinga, wanda kanin Shehu ne) da Sarkin Musulmi Muhamamdu Bello (dan Shehu Usman). Wannan takaddama ta janyo musayar ra’ayi tsakanin manyan malaman guda biyu, kuma suka yi bajekolin hujjoji, inda shi Shehu Abdullahi ya rubuta al Ghayth al Wabl fi sirat imam al adl, Shi kuma Bello yayi masa raddi a littafin sa Usul al Siyasat da kuma a cikin Infakul Maisur. Duk da yake rashin jituwa ce ta hujja ba ta kai ga yaki ba, amma ba a samu jituwa tsakanin Sultan Bello da kawun na sa ba sai bayan Yakin Kalambaina. Wanda shi ne ya zama sanadiyar sulhu a tsakanin su.

Tun zamanin Shehu Usman na da rai, Shehu Abdullahi, Shi ke rike da mukamin Waziri a daular, wannan rikici ya sanya, daular ta zauna babu waziri, har sai da aka samu sasanto a tsakani.

A sanadiyar wannan sasanto ne, Shehu Abdullahi ya samu damar zuwa Sakkwato domin ziyarar kabarin dan’uwan sa, kuma da zai koma sai Sarkin Musulmi Bello ya yi masa rakiya. A wannan rakiya ne, da za a yi sallama a shekarar 1817 Shehu Abdullahi ya cire alkyabbar sa ta wazirci, ya yafa wa Malam Gidado, kuma tun daga nan ya zama wazirin Sakkwato, har zuwa lokacin da ya ajiye mukamin a shekarar 1843, saboda sabani da ya taso tsakanin sa da Sultan Abubakar I.

Wazirin Sakkwato Gidado ya taka rawar gani wurin tabbatar da Daular Usmaniyya a kan dugaduginta, yayi karfin da ya kan iya zartar da hukunci ba tare da ya nemi izinin Sarkin Musulmi ba. Da irin wannan ne ma ya kwabe Sarkin Daura Ishaku ya nada dan sa. Shi ne ya jagoranci rundunar Fulani a lokacin da Daular Borno ta yi barazanar kai wa Kano hari. Kuma shi ya yi uwa ya yi makarbiya wurin sasanta sultan Bello da sheikh el Kanemi. Shi ne kuma kakan shehin malamin nan, wato Gidado bin Mustapha, wanda Heinrich Berth ya ambata kuma ya zauna ya kwashi ilmi a wurin sa a yayin da ya ziyarci Sakkwato. Gidado Shi ne mijin Nana Asmau bint Fodio.

Anya kuwa ace wannan kasurgumin malami ya rubuta tatsuniya?! A dai sake dubawa.

Allah ya jikan sa, ya yafe kurakuran sa, ya karbi jihadin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *