Yadda mafarauci ya hallaka ahalinsa a Anambra

Daga WAKILINMU

Rahotanni daga yankin Amanuke a karamar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra, sun nuna wani mafarauci mai suna Uchechukwu Nweke, ya harbe matarsa Mrs Patricia da bindiga har lahira sannan ya banka wa gidansu wuta tare dansa Mr Obinna a ciki a bisa dalilan da ba a kai ga ganowa ba.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar CSP Haruna Muhammed ya tabbatar da aukuwar lamarin. Inda ya ce wanda ake zargi, ya aikata ta’asar ne a safiyar Alhamis, 28 ga Janairun 2021 kana daga bisani shi ma ya harbe kansa.

CSP Muhammed ya ce, “‘Yan bijilantin yankin ne suka kawo musu rahoton abin da ya faru inda Nweke mai shekara 65 ya hallaka matarsa ‘yar shekara 55 da bindiga. Bayan haka, ya kona gidansu tare da wani dansa Obinna dan 29 a ciki, kana daga bisani ya harbe kansa da bindigar da ya hallaka matar tasa da ita.

“Jami’anmu na ofishin ‘yan sanda da ke Achalla sun ziyarci wurin da abin ya faru, inda suka kwashi mutane ukun da ibtila’in ya shafa zuwa asibitin da ke kusa wanda a nan ne aka tabbatar sun mutu baki dayansu.”

Ya ci gaba da cewa, “An adana gawarwakin a nan asibitin domin a yi musu ‘yan gwaje-gwaje, yayin da kuma an soma gudanar da bincike don gano sababin faruwar hakan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *