Inganta fannin lafiya shi ya fi muhimmanci ga Nijeriya bisa ga sayo rigakafin korona – Gates

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hamshakin dan kasuwar nan na Kasar Amurka, Bill Gates, ya shawarci Nijeriya da ta karkatar da hankalinta zuwa ga inganta fannin lafiyarta maimakon kashe makudan kudade wajen sayo allurar rigakafin cutar korona.

Gates ya ba da shawar ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai ta bidiyo a Talatar da ta gabata, inda ya yi kira ga Nijeriya da kada ta yi amfani da ‘yan kudaden da ta ware don kula da fannin lafiyarta wajen sayen rigakafin COVID-19 mai tsadar gaske.

Jaridar Manhaja ta kalato dan kasuwar na cewa, “Ina mai bada shawarar a bai wa fannin lafiya muhimmanci tare da wadata shi da kayayyakin aiki. A bayyane yake cewa ni ba dan Nijeriya ba ne, saboda haka zabi ya rage ga Nijeriya. Shawarta a nan ita ce, tsarin kula da lafiya a matakin farko shi ya fi komai muhimmanci, don haka ya kamata Nijeriya ta bada fifiko wajen inganta shi.

“Ina nufin mace-macen da akan samu saboda rashin ingancin tsarin kula da lafiya na matakin farko sai karuwa yake duk shekara fiye ma da yadda annobar korona ke kisa a fadin Afirka. Don haka ina fatan kowa a cikin al’umma ya kalli wadannan matsalolin kiwon lafiya da idon basira don a gyara.”

A cewar Gates, “Ya kasance Nijeriya ta samar da rigakafin da zai wadaci kasa baki daya, sannan akwai bukatar samun tsare-tsaren kula da lafiya masu nagarta saboda kare rayukan dimbin ‘yan kasa.”