An kashe naira miliyan 900 wajen samar da manhajar sayar da tikitin jirgin kasa – Amaechi

Daga WAKILIN MU

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa an samar da dandalin sayar da tikitin jirgin kasa ta intanet na Hukumar Jiragen Kasa ta Nijeriya (NRC) a kan kudi naira miliyan 900 ta hanyar wata yarjejeniya ta shekara 10.
Ministan ya bayyana haka ne kwanan nan sa’ilin da ya ke kaddamar da manhajar sayar da tikitin, ya na mai cewa hakkin kula da manhajar zai kasance ne a hannun wadanda aka yi yarjejeniyar da su na tsawon shekara 10, kana daga bisani ta koma karwashin kulawar NRC.

A cewar sa, samun manhajar babban cigaba ne ga hukumar NRC da Ma’aikatar Sufuri da kuma Gwamnatin Tarayya.

Amaechi ya ce, “Wannan aiki wanda haxin-gwiwa ne tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa, an shafe sama da shekaru uku ana aiwatar da shi wanda ya shafi hukumar NRC da NITDA, sannan a karshen lamari aka samu amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya.”

Ya ci gaba da cewa, “Yau shi ne farkon zamanantar da sayar da tikiti a dukkanin manyan tashohin zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna. Kuma wannan cikakken tsari ne wanda zai bada damar sanya ido kan sha’anin sayar da tikiti.

“Na yi amannar cewa wannan tsari daidai ya ke da tsarin sayar da tikiti mafi inganci a sassan duniya wanda zai taimaka wajen hana bata lokaci da inganta sha’anin sufuri da karfafa tattalin arzikin kasa gami da toshe duk wata kafa ta sulalewar kudaden gwamnati.”

Har wa yau ya ce, “Wannan tsarin shi ne ya fi dacewa musamman a wannan lokaci da ake fama da annobar korona, saboda tsarin zai taimaka wajen takaita cinkoson jama’a a tashoshin jirgin kasa kasancewar ko a kwance a gida, ko a wajen aiki mutum na iya sayen tikitin sa hankali kwance ta hanyar amfani da wayar sa.”

A karshe, ministan ya yi amfani da wannan dama wajen mika godiyar sa ga kamfanin ‘SecureID Limited’ da aka yi wannan yarjejeniya da shi, ya na mai cewa dukkan tsare-tsaren da za a samar wadanda ake sa ran su taimaka ne wajen inganta sha’anin sufurin jiragen kasa don cin moriyar fasinjoji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *