12
Mar
Daga IBRAHIM SHEME Kwanan nan Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya jawo wata muhawara a kan batun a yafe wa ‘yan bindiga ko a kashe su idan an gan su. Matsayar sa ita ce kada a yi wani zaman tattaunawa da su don a samu hanyar da za a warware ibtila’in kashe-kashe da ke faruwa a yankin Arewa-maso-yamma na ƙasar nan. Gara a nuna masu ƙarfin soja, a murƙushe su, babu sassautawa ko jinƙai. A wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon BBC, El-Rufa’i ya bayyana cewa duk wata hanyar lalama da za a bi…