’Yan bindiga: A yafe ko a bindige?

Daga IBRAHIM SHEME

Kwanan nan Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya jawo wata muhawara a kan batun a yafe wa ‘yan bindiga ko a kashe su idan an gan su. Matsayar sa ita ce kada a yi wani zaman tattaunawa da su don a samu hanyar da za a warware ibtila’in kashe-kashe da ke faruwa a yankin Arewa-maso-yamma na ƙasar nan. Gara a nuna masu ƙarfin soja, a murƙushe su, babu sassautawa ko jinƙai.

A wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon BBC, El-Rufa’i ya bayyana cewa duk wata hanyar lalama da za a bi domin a kawo ƙarshen kashe-kashen da ‘yan bindiga ke aikatawa ba za ta yi aiki ba. Ya ce duk wani mai faɗin wai a zauna a yi taro da waɗannan makasan domin a ji abin da ke damun su, a magance masu shi, kawai ya na ɓata wa kan sa lokaci ne. Ya yi nuni da cewa Bafillacen da a da bai fi ya samu N100,000 wajen kiwon shanun sa ba yanzu ya na karvar miliyoyin naira a vagas ba zai taɓa yarda ya koma rayuwa irin ta da ba. Babu hanyar da ta fi dacewa kamar a gama da shi kawai, inji shi.

Wannan matsayin da gwamnan ya hau, ya sava wa na wasu daga cikin abokan sa gwamnoni, musamman na Zamfara da na Katsina, wato Bello Matawalle da Aminu Bello Masari. Su a ganin su, hanya mafi dacewa ita ce a zauna da maharan nan a yi sulhu. “A matsayi na na gwamna, abu mafi muhimmanci a gare ni shi ne in tabbatar da na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, sannan in tabbatar da cewa mutane na kwana da idanun su biyu a rufe,” inji Matawalle.

Mai ɗaki dai shi ya san inda ruwa ke zubo masa. Don haka Matawalle da Masari sun san inda bakin zaren ya ke. Su aka fi sanya wa ido; mutanen su aka fi kashewa. Su ake damu da matsalar rashin tsaron, har wasu na cewa sun gaza. Shi ya sa tuni su ka yi nisa wajen tattaunawa da ‘yan bindiga domin su samu sa’ida.

To amma fa shi ma El-Rufa’in ya san bakin zaren. Shi ma jihar sa na daga cikin jihohin da ‘yan bindiga su ka fi yin ɓarna. Kuma a zato na shi ma ya bi hanyar lalamar, ya ga ba ta vulle ba. Ya ga babu hanyar da ta fi dacewa sai a gurza da maharan, a ga wanda za a kayar. Ra’ayin El-Rufa’i ɗaya ne da na takwaran sa na Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello. A cewar sa, yi wa ‘yan bidiga yadda su ke so zai ƙara iza wutar hare-haren da su ke kaiwa ne kawai.

A nazarin da na yi, yawancin ‘yan Nijeriya sun fi yarda da matsayin da su Malam El-Rufa’i su ka hau game da wannan al’amari. Abin da jama’a ke cewa shi ne a ina aka tava ganin an yi sulhu da ɓarawo ya dawo da kaya ko kuma ya daina sata? Idan ka ga ɓarawo ya tuba, to ya ga uwar bari ne. Ko dai tsufa ya kam masa, ko kuma ya ji baƙar wuya daga nauyin ikon hukuma.

Waɗannan mahara ba su da bambanci da gawurtattun ɓarayi. Babu batun tuba a wajen su. Dalili shi ne sun lasa sun ji da zaƙi; sun latsa sun ji taushi. Irin caɓawar da su ke yi a daji da cikin gari ta ba su damar samun wata irin rayuwa wadda a da ba su san akwai irin ta ba. Rayuwa ce ta cin bilis: ga kuɗi, ga abinci da nama, ga mata. Uwa-uba, ga babban makami wanda ke ba su ƙarfin zuciya da ƙudirin cewa sun fi soja.

A daji, sun kafa gwamnatin su wadda ba ta bin doka ko oda da aka sani. Su ke yi wa kan su doka da oda. Su auka wa gari, su kashe na kashewa, su kamo wanda su ka ga dama, su tursasa biyan diyya a kan dangin wanda su ka kama; wani lokacin ma ko an biya diyyar sai su halaka wanda ke tsare a hannun su. Su yi wa mata fyaɗe. Su azabtar da ƙananan yara, su jefa dattijai cikin uqubar da a da ana zaton sai a lahira kaɗai ake samun ta.

Babban tu’annatin da ‘yan bindiga su ka fi janyowa shi ne barbaɗa fargaba a zukatan mutanen da ke yankunan da ake wannan tashin-tashinar. Kusan kowa na barci ne da ido ɗaya, zuciya cikin ɗarɗar. Haka ake kwana ana tashi a cikin tsoron abin da ka je ya dawo. Duk wani mai ɗan hannu da shuni a karkarar da ake bala’in bai iya kwana a gida. Akwai masu guduwa zuwa wani garin su kwana, su dawo gida da safe.
Kai, da rana ma ba a huta ba. Manomi bai iya zuwa gona ya yi aiki cikin kwanciyar hankali. Shi da ‘ya’yan sa cikin tsoro su ke, domin an sha zuwa har gona a kama mutane, kuma a bindige wasu.

Ina jami’an tsaro? Akwai mazan fama, to amma su ɗin ma akwai fargaba tare da su. An sha kai masu farmaki ana kashe su, har ma a kama na kamawa. Dalili shi ne yawan su bai isa ba, makaman su ba su isa ba, sannan ba su da cikakkiyar masaniya game da abin da ‘yan bindiga su ke ciki. Ko gwabzawa su ka yi da maharan, da qyar su ke yin galaba. Har ta kai ga mutanen karkarar da bala’in ke aukuwa su na ganin cewa jami’an tsaro ba su iya kare su yadda ya kamata.

Gazawar da hukumomin tsaro su ka yi ce ta sa wasu gwamnonin, har ma da malamai irin su Dakta Ahmad Gumi, su ke cewa a yi sulhu da ‘yan bidiga shi ya fi. In da a ce jami’an tsaro za su iya kawar da duk wani ɗan bindiga ko su kamo shi su kai shi kotu, to da ba za a ce a yi sulhu ba.

Ni ra’ayi na kenan. In dai za a iya kama masu laifin, to batun sulhu bai taso ba. Wane sulhu za a yi da mutumin da ya ɗau rai, ya saci kuɗi, ya yi fyaɗe, ya hana jama’a kwanciyar hankali? Idan an yi sulhu da shi, ai an ɗaure wa ƙarya gindi ne; an ba wasu damar su ma su ɗau makamai su shiga daji. Amfanin hukunci shi ne ya tsoratar da duk wani mai tunanin aikata laifi.

Saboda haka haƙƙin da ya rataya a wuyan hukumomi shi ne su tabbatar da tsaro ta hanyar murƙushe masu jawo fitina. Duk wanda aka kama, a kai shi kotu ta hukunta shi, ba wai a bindige shi ba kamar yadda wasu ke cewa, in dai ba  wajen musanyar wuta ba ne.

Abin tambayar shi ne shin gwamnati za ta iya daƙile ‘yan bindigar kuwa? Ina isassun ma’aikatan? Ina isassun makaman, kuma na zamani? Idan babu waɗannan, to ganin bayan ‘yan bindiga zai yi wahala. Za a yi ta ɗauki-ba-daɗi da su na tsawon shekaru. Idan har ba za a iya murƙushe su ba, to talakan da abin ya fi shafa zai so a zauna da su a ba su haquri da kuɗi, domin fa shi babu abin da ya fi so kamar rayuwar sa ta koma yadda ta ke a da. A wurin sa, Turancin ya isa haka.