Ciwon daji: An damu da shi kuwa?

Daga IBRAHIM SHEME

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 4 ga Fabrairu ta kowace shekara a matsayin Ranar Yaƙi Da Cutar Daji ta Duniya, wato a turance ‘World Cancer Day’. Muhimmancin ranar shi ne mutane su tuna da irin ɓarnar da cutar ke yi da matakan da ya kamata a ɗauka don rigakafi da kuma hanyoyin magance ta. A jiya Alhamis ne wannan rana ta kama a bana.

Abin mamaki, ban ji inda aka yi wata yekuwa ko gangami don tunawa da ranar ba a jiya. Akwai ‘yan labarurruka da ƙungiyoyi masu yaƙi da cutar su ka ɗan yaɗa, su ɗin ma ba sosai ba. Ta yiwu hakan ya faru ne saboda a yau babu cutar da ta damu jama’a kamar korona, wadda ke ta ragargazar rayuka a kowace nahiya.

To, kada mu shafa’a, ciwon daji ma ciwo ne mai kisa. Akwai masu fama da shi, kuma su a wajen su ya ma fi korona.

Da farko ma dai, mecece cutar daji? Ya ake ta na kama mutane? Binciken da na yi ya nuna mani cewa cutar daji kan faru ne a lokacin da aka samu sauyi a yanayin ƙwayar jini na jikin mutum, wato ‘cell’. Idan ƙwayar ta sauya, ta lalace, to kuma sai ta fara yaɗuwa a cikin jiki, daga nan sai ta zama cuta.

Ciwon daji kala-kala ne, sun fi ɗari. Kuma ya kan kama sassan jiki daban-daban. Waɗanda aka fi sani su ne: ciwon daji na nono; ciwon daji na hanji; ciwon daji na mahaifa; ciwon daji na fatar jiki; ciwon daji na babban hanji; ciwon daji na huhu; ciwon daji na cikin jini; ciwon daji na ƙwayoyin halitta; ciwon daji na dubura, da ciwon daji na mashimfiɗin fatar jiki.

Hanyoyin gane ciwon daji na farko sun haɗa da kumburi, fitar jini da ba a saba gani ba, ramewa babu dalili, da sauyi wajen yin bahaya. Likitoci sun ce duk da yake waɗannan alamun za su iya kasancewa na wani ciwon daban, amma za su iya kasancewa na ciwon daji.

Su wa ciwon daji ya fi kamawa? Masana sun ce ciwon na iya kama ko ma waye, to amma an fi zaton sa ga mashaya taba, da masu ƙiba, da marasa abincin kirki, waɗanda ba su motsa jiki, da masu yawan shan giya. Sannan ya na kama masu wasu cututtukan (misali HIV/AIDS), da waɗanda su ka shaƙi wani sinadari na masana’anta. Ana kuma gadon ciwon.

Haɗarin kamuwa da ciwon daji ya fi shafar masu yawan shekaru, sannan ya fi kama mutane a ƙasashen da su ka ci gaba. To amma mu ma a Afrika cutar na ƙaruwa saboda sauyawar rayuwa ta zamani.

Kuma fa kada mu ɗauka cewa cutar ba ta kama ƙananan yara. A cikin 2012, kimanin yara 165,000 da ba su kai shekara 15 da haihuwa ba cutar ta kama.

Saboda haka mutum na iya ɗaukar matakai da su ka haɗa da daina shan sigari, motsa jiki maganin mummunar ƙiba, daina shan barasa, cin abinci mai gina jiki tare da ganyayyaki da kayan lambu, allurar rigakafin kamuwa da wasu cututtuka, rage cin naman shanu da naman gwangwani da aka yi a ma’aikata, kauce wa shaƙar hayaƙi ko wata iska da ke fitowa daga wata ma’aikata, sannan ana so mutum ya rage zama cikin zafin rana kai-tsaye.

Yaya mutum zai yi ya magance ciwon daji? Da farko dai, ana so mutum ya riƙa yin gwaji jefi-jefi. Misali, ana so mata su je a riƙa auna nonon su da wata na’ura ta musamman mai bincikar farkon kamuwa da ciwon daji. Ta wannan hanyar ne za a iya gano farkon shigar cutar saboda a tashi tsaye haiƙan wajen magani. Ana yin maganin ne ta hanyoyi na zamani a asibiti, wanda ya haɗa da yi wa mutum tiyata don a ɗebe inda cutar ta kama, da ba shi magani. A ƙasashe irin namu kuma, akwai masu bada maganin gargajiya waɗanda ke faɗin su ma maganin su ya na aiki.

Masana sun ce warkewa daga ciwon daji ya danganta da abubuwa da dama: yaushe cutar ta kama mutum, zurfin kamuwar, irin wurin da ta kama, da sauran su.

Idan mun dubi alƙaluman ciwon daji a faɗin duniya da ma nan Nijeriya, abin ya na da ban-tsoro. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce a yau akwai masu fama da ciwon daji su miliyan 43.8 a duniya, kuma a duk shekara ana samun sababbin waɗanda su ka kamu su sama mutum miliyan 18. A yau, ciwon daji na kashe mutum 1 a duk cikin mutum 6 a faɗin duniya, wanda ya kama mutum miliyan 9.6 ke mutuwa daga ciwon daji a shekara.

Abin baƙin ciki shi ne, kashi 70 cikin ɗari na mace-mace daga ciwon daji su na faruwa ne a ƙasashe masu tasowa irin Nijeriya. A wani rahoto da na gani jiya, an ce akwai sama da mutum 200,000 da ke fama da ciwon daji a Nijeriya, sannan ana samun sama da mutum 100,000 da ciwon ke kamawa a duk shekara. Rahoton ya ce sama da ‘yan Nijeriya 200 ne ke mutuwa a sanadin ciwon daji a kullum, kuma a cikin waɗannan ɗin, 32 mata ne da ke mutuwa daga ciwon daji na nono, yayin da 28 ke mutuwa daga ciwon daji na mahaifa.

A cikin 2010, an ƙiyasta cewa ana kashe zunzurutun kuɗi har dalar Amurka tiriliyan 1.16 a duk shekara wajen magance ciwon daji.

Majalisar WHO ta ce idan abin ya ci gaba da tafiya a haka, to masu kamuwa da ciwon daji za su ƙaru da kashi 60 cikin ɗari nan da shekara ashirin, kuma kashi 80 cikin ɗari na waɗannan daga ƙasashe masu tasowa irin namu za su fito. An ce wannan ƙiyasin ma zai iya ƙaruwa idan aka yi la’akari da yadda hankalin yaƙi da cututtuka ya koma ya karkata zuwa yaƙi da cutar korona.

Abin damuwa shi ne yadda aka bar Nijeriya a baya wajen yaƙi da ciwon daji. Mutane ƙalilan ne ke fafutikar nemo hanyoyin da za a bi a yaƙi cutar. Ɗaya daga cikin irin waɗannan mutanen ita ce uwargidan gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Umaru Shinkafi Bagudu. Akwai kuma Dakta Abia Nzelu, babban sakataren kamfanin GivingTide International. Waɗannan mutanen sun cancanci yabo kan yadda su ke amfani da lokacin su da dukiyar su wajen jawo hankali don a gane halin da ake ciki don a yaƙi cutar. Su na daga cikin masu gudanar da shirin yaƙi da ciwon daji na ƙasa, wato ‘National Cancer Prevention Programme’ (NCPP), wanda wasu ƙungiyoyi masu zaman kan su ke gudanarwa. Tun daga 2007, shirin na NCPP ya ke jagorantar yadda za a yi rigakafin cutar daji a Nijeriya. Hoɓɓasan su ya rage mace-mace sanadin cutar daji a nan ƙasar daga 75,392 a 2008 zuwa 70,327 a 2018 kamar yadda alƙaluman WHO su ka nuna.

Ya kamata Nijeriya ta yi koyi da ƙasashen Indiya da Masar inda ake da manya da ƙananan asibitoci na musamman da ake kira ‘Comprehensive Cancer Centre’ (CCC) da aka gina domin yaƙi da cutar daji. Misali, a yayin da Indiya ke da asibitocin CCC sama da 200, mu a Nijeriya ba mu da ko ɗaya. Masar, mai yawan mutane miliyan 82.5, ta na da babbar cibiya mai suna ‘National Cancer Institute’ (NCI), da kuma asibitocin CCC da dama. Sannan Masar ta na da asibitin cutar daji na ƙananan yara mafi girma a duniya, wato ‘Children’s Cancer Hospital Egypt’ (CCHE).

Saboda haka, tilas ne mu bai wa cutar daji muhimmancin da ya kamace ta a Nijeriya, domin akwai ɗimbin masu fama da ita, kuma za ta iya kama kowa idan tsautsayin ta ya faɗa kan shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *