CBN ya haramta wa bankuna hada-hadar kuɗaɗen intanet

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bai wa bankuna umarnin su rufe duk wani asusun ajiya da karɓar kuɗaɗe a banki da ke da alaƙa da cinikin kuɗin intanet (cryptocurrency).

A Juma’ar da ta gabata CBN ya aike wa bankunan umarnin nasa zuwa bankuna masu karɓar ajiyar kuɗaɗe (DMB) da hukumomi masu hada-hadar kuɗaɗe (NBFI) da makamantansu, a kan su gaggauta daƙile dukkan asusun da ake amfani da su wajen hada-dahar kasuwar sulallan intanet (bitcoin).

Idan dai za a iya tunawa a Janairun 2017 ne CBN ya bayyana cewa ana amfani da hada-hadar kuɗaɗen intanet irin sulallan bitcoin da litecoin da danginsu wajen tallafa wa harkokin ta’addanci da tafka zambar kuɗaɗe. Tare da cewa dokar ƙasa ba ta halasta yin amfani da nau’in waɗannan kuɗaɗe a Nijeriya ba.

Don haka CBN ya ce yana tunatar da bankuna da sauran hukumomi masu hada-hadar kuɗaɗe cewa mu’amala da kasuwacin waɗannan sulalla haramun ne.

Daraktan Sashen Sanya wa Bankuna Ido Bello Hassan, da takwaransa mai kula da sha’anin biyan kuɗaɗe Musa Jimoh, su ne suka sanya wa umarnin da CBN ya fitar hannu a Juma’ar da ta shige.

CBN ya nuna nan take yake buƙatar bankuna da hukumomin da lamarin ya shafa su zartar da umarnin nasa. Yana mai cewa duk bankin ko hukumar da ta ƙi yin biyayya ga wannan umarni, za a saka mata takunkumi.

A hannu guda, shugaban cibiyar canjin kuɗaɗe a kasuwar sulallan intanet (Binance) Changpeng Zhao, ya maida martani ga umarnin da CBN ya bayar na haramta wa bankuna da danginta mu’amala da harkarsu.

A cewar Zhao, wannan mataki da CBN ya ɗauka zai yi wa hada-hadar naira illa, inda ya shawarci masu harkar kasuwancin sulallan da su hanzarta kwashe kuɗaɗensu gudun kada su tafka hasara kamar dai yadda ya wallafa a shafinsa na tuwita a ranar Juma’a.