Amnesty International na neman wargaza Nijeriya – inji Lai Mohammed

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Tarayya ta zargi Ƙungiyar Kare ‘Yancin Ɗan-Adam ta Duniya (AI) da take-taken neman wargaza Nijeriya da gangar ta hanyar ɗora zarge-zarge a kan gwamnati da kuma sojoji.

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya yi wannan zargi yayin wata hira da wata tashar talabijin ta yi da shi a Juma’ar da ta gabata a Legas wadda Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN) ta bibiya.

Ministan ya bayyana haka ne a matsayin martani ga wani rahoton ƙungiyar a kan yaƙi da batun take ‘yancin ɗan-Adam a faɗin duniya inda ta nuna an yi zargin an kashe mutane da dama yayin zanga-zangar EndSARS a Lekki, jihar Legas, a cikin Oktoban 2020.

Ƙungiyar ta zargi gwamnatin Nijeriya da yin rufa-rufa wajen kula da batun kisan da aka yi zanrgin an yi inda ta yi kira da a kama tare da hukunta ɗaya daga cikin tsoffin manyan hafsoshi a Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) bisa zargin take ‘yancin ɗan-Adam.

Da yake bayani a cikin shirin, Lai ya ce kamar sauran ƙungiyoyi, ita ma AI ta gaza gabatar da ƙwararan shaidu da za su tabbatar da cewa lallai an kashe mutane a Lekki a wancan lokaci da hatsaniyar ta auku.

A cewar Lai, “Muna ƙalubalantar Amnesty International idan tana da ƙwaƙƙwarar shaida kan abin da ta take zargi ta fito ta gabatar da ita tare da bayyana sunayen da adireshin waɗanda aka ce an kashe a ƙofar shiga gari a Lekki.

“Gaskiyar batu shi ne, wata ƙungiya mai zaman kanta ƙarƙashin jagorancin AI ta yi ta yaɗa labarun ƙarya game da abin da ya faru a Lekki.”

Ya ci gaba da cewa hanya mafi dacewa wajen tabbatar da an kashe mutane a Lekki, shi ne bayyana a gaban kwamitin binciken da gwamnatin Legas ta kafa don yin bayani.

“Sama da kwanaki 100 da kafa wannan kwamiti, amma har yanzu ba a samu wanda ya fito ya ce ɗana ko ‘yata ta tafi wajen zanga-zangar amma ba mu ga dawowar ta/sa ba.

“Amnesty International ba ta girmama tsarin shari’armu in ba haka ba da sai ta bada shaida a gaban kwamitin bincike maimakon yaɗa labarun ƙarya…”, inji Lai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *