INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Nijeriya kafin zaɓen 2023 – Mahmood Yakubu

Daga WAKILIN MU

Nan da lokacin da za a gudanar da babban zaɓe a Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta samar da ƙarin mazaɓu a faɗin ƙasar.
 
Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar (IVEC), Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a cikin Agustan 2014 INEC ta gabatar da buƙatar samar da ƙarin mazaɓu 30,027, inda arewacin ƙasar za ta samu mazaɓu 21,615 yayin da kudu za ta samu 8,412.
 
Wannan ya janyo ce-ce-ku-cen da ya sa INEC ta watsar da shirin.
 
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa a halin yanzu Nijeriya ba ta da isassun mazaɓu.