Mafarin matsalar Fulani da yadda za a magance ta (I)

Daga FARFESA UMAR LABDO

Shimfiɗa
Ina yin wannan rubutu a matsayina na Babban Sakataren ƙungiyar FULDAN na ƙasa. FULDAN (Fulani Development Association of Nigeria) ƙungiya ce mai fafutuka don ci gaban Fulani a fagagen ilmi, al’adu, tattalin arziki da zamantakewa. An kafa ta a shekarar 1999, tana da wakilci a yawancin jihohin ƙasar nan kuma tana da alaƙa da ƙungiyoyi takwarorinta a ƙasashe makota. Ƙungiyar tana shirya tarukan wayar da kan Fulani da koya musu sana’o’i da sabbin dabarun kiwo don inganta sana’arsu. Haka nan tana gudanar da azuzuwan yaƙi da jahilci da koyon addini a rugage da ƙauyukan Fulani.

Gabatarwa
Al’ummar Fulani an san su da kunya, kawaici, kara da son zaman lafiya. Mutanen da suka fi kowa sanin Fulani a ƙasar nan, watau Hausawa, a harshensu Fulatanci yana nufin kunya da kamun kai. Misali, idan mutum ya je baƙunta wani gida, aka ba shi abu ya ki karɓa, sai a ce “kada ka yi fulatanci” ko “kada ka yi pulaku”.

Fulani sun zauna da kowa a ƙasar nan zaman lafiya da girmama juna. A tsawon ɗaruruwan shekaru, babu wani yanki ko ɓangare na ƙasar nan da Fulani ba su zauna ba, haka nan babu wata ƙabila ko jinsi da Fulani ba su maƙotata ba. Amma a ‘yan shekarun nan, al’amura sun sauya. Bafulatani wanda aka sani da zaman lafiya, inda duk ya je ana maraba da shi, a yau shi ne ɗan tashin hankali, kuma inda duk ya wuce sai ana kyarar sa. Fulani da yawa mazauna karkara da dazuka sun shiga aikata laifi, musamman fashi da makami, satar dabbobi, garkuwa da mutane don neman fansa, da sauransu. Mene ne abinda ya faru? Me ya kawo sauyi a halayyar Fulani da aka san su da ita a ɗan ƙanƙanin lokaci?
Dalilan da suka sa Fulani Ɗaukar Makami.

Akwai dalilai guda huɗu da suka sauya rayuwar Fulani da halayensu har suka kai su daga ƙarshe ga ɗaukar makami da aikata laifi. Dalilan sun haɗa da:

■ Soke jangali. Wannan shi ne dalili na farko da ya fara warware tufkar Fulani da sakwarkwata rayuwarsu. ‘Yan siyasa da suka soke jangali a zamanin jamhuriya ta biyu (1979 – 1983) bisa dukkan alamu sun yi haka ne da kyakkyawar niyya amma abin daga baya ya zama sharri ga Fulani. A lokacin da Fulani suke biyan jangali su ‘yan gatan gwamnati ne. Hukuma tana kula da su saboda maƙudan kuɗaɗe da suke biya a duk shekara. Don haka ana kula da lafiyar dabbobinsu, ana kula da burtalolinsu da laɓukansu, babu wanda zai toshe hanyoyin da suke wucewa da shanunsu. Amma bayan da aka soke jangali gwamnati ta yi watsi da su, saboda a yanzu babu wani amfani da suke tsinana mata. Sai ya zama al’amuran Fulani sun fara ci baya. Babu wanda ya kula da haƙƙoƙinsu da muradunsu da maslahohinsu. Ko kuka suka kai, ko ƙorafi, ba safai ake sauraron su ba. Rashin ilmi da wayewa, da rashin kyakkyawan shugabanci, ya ƙara sanya lamarin ya ta’azzara.

■ Dalili na biyu shi ne zuwan siyasa daga shekarar 1999. Kamar yadda aka sani, Bafulatanin daji ba ya zama wuri ɗaya, saboda haka ba ya ƙuri’a balle zaɓe. Wannan ya sa ba shi da wani amfani ga ɗan siyasa wanda shi ƙuri’arka ce darajarka a wajensa. Saboda haka, ‘yan siyasa ba sa lissafi da Fulani sam, idan ma ka ji sun ambace su to sai dai saboda tsurku na ‘yan siyasa. Koda rigima ta faru tsakanin manoma da makiyaya, to shi ɗan siyasa yana ɓangaren manoma. Ta sha faruwa jami’an tsaro su kama manoma da makiyaya saboda wani hargitsi ko tashin hanjali, idan ‘yan siyasa suka je sai su karɓo manoma, su makiyaya kuwa sai dai shanunsu su fiddo su, watau su sayar da saniya su ba da cin hanci. To ka ji yadda siyasa ta ƙara damalmala al’amarin Fulani makiyaya.

■ Dalili na uku shi ne bayyanar takin zamani da karɓuwarsa a wajen manoma. Kafin zuwan takin zamani manomanmu sun dogara da takin dabbobi wajen nomansu. Manoma su ke gayyatar makiyaya su zo su shekare a gonakinsu bayan sun girbe amfanin don su samu taki. A wancan zamanin alfarma ce Bafulatani ya yarda ya shekare a gonarka da dabbobinsa. Amma bayan takin zamani ya samu karɓuwa a wajen manoma sai suka wayi gari ba sa buƙatar kashin saniyar Bafulatani, wanda hakan ya rage kimar Fulani ta tattalin arziki. Sai ya zama Fulani, waɗanda a da sai sun yi yanga suke amsa gayyar manoma su zauna a gonakinsu, a yanzu manoma ne yake musu yanga da tsiya. Sai ka ji manomi ya ce da makiyayi “ba na buƙatar kashinka” kashin saniya yake nufi fa, amma sai ya ce kashinsa saboda iya shege. A yanzu maimakon manoma su yi zawarcin makiyaya, korar su suke yi.

■ Dalili na huɗu, kuma mafi haɗari, shi ne yadda jami’an tsaro suka gane Fulanin daji. Sun gane cewa makiyayan nan dai jahilai ne gidadawa, ba su san shari’a ba, ba su san haƙƙi ba ko yadda ake ƙwato shi. Saboda haka sai jami’an tsaro na ko wane fanni, sojoji da ‘yan sanda da mobayil da sauransu, suka mayar da Fulani makiyaya wata ‘yar gayauna inda ake zagawa lokaci zuwa lokaci ana samun na cefane idan wata yai nisa. Tun ana abu kamar wasa, idan rikici ya faru tsakanin makiyaya da manoma, an tura jami’an tsaro su je su kashe wuta, sai kawai su kori kare a gindin ɗinya. Sai su ƙwace shanun makiyaya su yi gwanjansu, su sa kuɗin a aljihunsu. Sannu a hankali al’amari ya zama “big business”. Sa’ad da duk wani abu kaɗan ya tashi, sai jami’an tsaro su yi wa Fulani dirar mikiya, su buɗe musu wuta, su kashe na kashewa su kori na kora, sa’an nan su loda shanu a manyan motoci sai kasuwa. Tun ana yin abu daga daji sai kasuwa, har manyan oga-oga na jami’an tsaro suka gano sabon fataucin, sai aka riƙa kai musu nasu kaso duk lokacin da dawa ya yi nama.

To a taƙaice dai, mai karatu, ka ji yadda aka koyawa Fulani makiyaya ta’addanci. Jami’an tsaro ne suka koya musu.
Sai dai ya kamata mu yi adalci. Ba jami’an tsaro ne kaɗai suka mayar da dukiyar makiyaya da rayuwarsu ganima ba. Akwai wasu masu laifin. Na farkonsu shugabannin wasu ƙungiyoyin Fulani waɗanda ya kamata a ce suna kare su, suna magana da yawunsu.

Irin waɗan nan yawanci suna haɗa baki da jami’an tsaro da wasu hukumomi kamar alƙalai, hakimai, dagatai da masu unguwanni, su karɓe shanun Fulani makiyaya ta hanyoyin zamba iri-iri waɗanda suka haɗa wani lokaci har da ɗauri da tara da barazana. Banda waɗan nan kuma, akwai ɓarayi masu satar shanu da ‘yan ta’adda da masu ƙabilanci waɗanda suke kashe Fulani suna ƙone gidajensu da bukkokinsu. Wannan ya sa Fulani makiyaya dukan yai musu yawa. Ko ina suka juya babu sa’ida. Babu shakka hakan ya taimaka wajen Fulani su yanke shawara cewa babu abinda ya rage musu sai su kare kansu.

‘Yan makonni baya kaɗan, gidan Radiyon Freedom Muryar Jama’a ya ba da rahoton irin wannan “big business”. Wasu ‘yan sanda ne dake aiki a Abuja suka haɗa baki da abokan aikinsu dake Kano. Sai su fito farautar Fulani a jihohin tsakiyar Nijeriya, kamar Kogi ko Nassarawa, idan suka kama Bafulatani sai su kawo shi wani caja ofis a Sabon Garin Kano, sai su ajiye shi a sel na tsawon makonni. Sai ya galabaita, can kuma ‘yan uwansa suna ta cigiya, sai su koma inda suka kamo shi, su yi cigiyar ‘yan uwansa. Idan suka same su sai su ce ɗan uwanku yana Kano, an kama shi da laifin ta’addanci, idan an gama binciki za’a kai shi Abuja.

Mun zo mu taimaka muku ne kada ku bari a kai shi Abuja,  domin idan an kai shi harbe shi za’a yi. Da zarar Bafillace ya ji zancen Kano da Abuja sai ya kama shanu ya sayar ya zo ya fanshi ɗan uwansa. A lokacin da Freedom Radio suka yaɗa wannan rahoto, hukumomin ‘yan sanda sun ce za su bincika, amma har yanzu ba mu ji kome ba.

To wannan shi ne mafarin matsalar Fulani wacce kowa yake magana a kai, wanda ya sani da wanda bai sani ba. Kowa yana ba da tasa shawara. Da mai cewa a yake su, a kashe su, da mai cewa a yi sulhu da su, a biya su diyya. Za ku ji namu ra’ayi a kashi na biyu na wannan maƙala, in Allah ya yarda.

Babban Sakataren Ƙungiyar Fuldan na Ƙasa. FULDAN (Fulani Development Association of Nigeria) ƙungiya ce mai fafutuka don ci gaban Fulani