Shin in Fulani makiyaya su ka fice daga Ondo salama ta samu?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA


Wa’adin da Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu, ya bai wa Fulani makiyaya su fice daga dazukan jihar sa, ya haddasa muhawara mai zafi tsakanin kudanci da arewacin Nijeriya. Muhawarar ta dogara ga yadda mai sharhi ko ra’ayi ya ke ganin abun.

Ga masu ɗaukar makiyaya ko Fulani makiyaya cewa ’yan Arewa ne ko ma ’yan’uwan su ko ma a ce su na dangantaka da Musulunci ko da ma a iya samun mabiya adddinin Kirista a cikin su da waɗanda ba su san ko “Ba Sin Mi Ara Ba…” to, za su ɗauki wa’adin da Akeredolu ya ba wa makiyayan a matsayin takalar faɗa da nuna bambancin ƙabilanci.

Ra’ayin ajin masu wannan tunani ya ƙara ƙarfi da fitowar jagoran matasan ’yan ɓangaren Yarbawa a Oyo, wato Sunday Igbaho wanda shi ma ya ba wa Fulani makiyayan wa’adin mako ɗaya su fice daga yankin Igangan na Ƙaramar Hukumar Ibarapa a Jihar ta Oyo, ko ma a taƙaice su fice daga Oyo kowa ma ya huta.

Haƙiƙa akwai waɗanda ke ɗaukar Fulani makiyayan a matsayin wa imma ’yan ta’adda ko masu mara wa ’yan ta’adda da ke satar mutane, kashe su ko yin fyaɗe baya. Don haka sun gamsu da matakin na Gwamna Akeredolu da Igbaho cewa daidai ne su kori miyagun iri daga yankin nasu.

Wannan dai ya zama an yi wa dukkan makiyayan da a zahiri ba su da ilimin boko balle na adddini kuɗin goro a matsayin mugayen mutane da ya dace a yi kukan kura a gama da su don aminta daga sharrin su.

Wannan muhawara na ɗaukar lamari na ƙabilanci da ɓangaranci da kuma ke ƙarewa a tsakanin manyan masu sharhi da siyasar 2023.

Tuni Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Ondo ba shi da hurumin korar wani daga wani sashe na jihar, domin dukkan ɗan Nijeriya yana da ’yancin zama a jihar da ya ke so.

Fadar Gwamnatin Nijeriya ta ce, “gwamnan ya dace ya magance miyagun iri ne ba sallamar dukkan nau’in wasu mutane daga jihar ba.”

Kazalika, an shiga musayar magana tsakanin Ƙungiyar Kare Muradun Yarbawa da ta Tuntuɓar Juna ta Arewa “ACF”.

Lamarin bai tsaya kan manyan ƙungiyoyin kare yankin ba, don hatta shugabannin ƙungiyoyin ƙabila ko keɓantacciyar sana’a sun shiga furta kalaman martani. Shugaban Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta “Miyetti Allah Kautal Hore” Bello Boɗejo ya ce sam makiyaya ba za su fice daga dajin Ondo ba, domin makiyaya na da haƙƙin zama a dukkan dazukan Nijeriya.

Boɗejo ya ce, “Fulani makiyayan sun fi shekaru 250 a dajin Ondo su na kiwo, don haka ba zai yi wu Akeredolu ya girma ya kori makiyayan da tun ba a haife shi ba su ke kiwon su a jihar.”

Bello Boɗejo ya ce, makiyayan kan zauna a daji duk hatsarin sa har ya samu albarkar da manoma za su shigo su yi noma. Ya ci gaba da cewa, ko da inci ɗaya makiyayan ba za su bar dazukan Ondo ba.

A ƙarshe, Boxejo ya yi alwashin kai ƙarar gwamnan kotu don dakatar da shi daga uzura wa makiyayan.

Shin martani ko ƙara ba da wa’adin cewa wasu su tashi daga wani yanki zai kai Nijeriya tudun mun tsira kuma an samu salama kenan? Idan makiyayan sun tashi ina za su nufa, ko Arewa za su dawo? Shin duk makiyayan ’yan Arewa ne kuwa ko ma ’yan asalin Nijeriya ne?

Gwamna Akeredolu na APC na Ondo, shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Yamma kuma ya na kan gaba wajen kafa ƙungiyar tsaro ta Yarbawa “AMOTEKUN” kuma ba ya sauraron zama a jam’iyya ɗaya da Shugaba Buhari wajen bayyana matsayar sa kan lamuran da suka shafi muradun Yarbawa.

Ya na da muhimmanci Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro su kashe wannan wutar tun ta na gaushi, domin idan ta tashi balbal sai Allah kaɗai Ya san wanda zai tsira daga harshen ta!.