Lokacin siyasa ne lokacin da na fi so – Farida Abubakar

Daga AISHA ASAS

Hajiya Farida Abubakar mace mai kamar maza, wadda ta ke da kishin neman na kanta ba tare da jiran miji ko iyaye sun yi mata hidimar ta ba, kuma macen da ta riƙi sana’ar gasa Burodi da hannu bibbiyu, wadda har ta kai ta matsayin da ta ke a yanzu. mace ce da ya kamata mata su yi koyi da ita, domin ta haɗa taura biyu a lokaci guda, wato aiki da kasuwanci. A wannan hirar da wakiliyar mu ta yi da ita, masu karatu za su ji yadda ta fara wannan sana’a.

Masu karatun mu za su so jin taƙaitaccen tarihin ki.
Suna na Farida Abubakar, na yi makarantar Firamare ɗina a Jabi daga nan na yi Sakandare ɗina a FGGC Bakori, na yi Difloma a jami’ar Abuja, yanzu haka kuma ina shekarar ƙarshe a Open University.

Hajiya wane irin kasuwanci ki ke yi kuma ki ka sa gaba yanzu?
To ni dai Baker ce, wato mai kasuwancin gasa Burodi, amma mu na yin kala-kala irin masu kwakwa da kuma wanda mutane su ka fi sani, kowane kala dai mu na yi.

Ga ki dai ke mace ce. Shin me ya ba ki sha’awar yin irin wannan sana’ar?
Kin san ita sana’ar abinci kusan in ce babu bashi a cikin ta, duk da dai babu wata sana’a da mutum zai yi da za a rasa ci mishi bashi, amma dai sana’ar da ta shafi harkar abinci akwai sauƙi sosai, saboda duk wanda zai zo ya ɗauka zai ba ki kuɗin ki nan take. To mahaifi na ya ga yara na sun fara tasowa sai ya kira ni ya ce min zaman nan fa ba zai yiwu haka ba yara na girma amma babu wata sana’a da na ke yi, domin ba a san yadda rayuwa za ta kasance ba. Saboda haka in zava karatu ko sana’a; idan kuma gabaɗaya zan haɗa duk zai tallafa min in cigaba da yi. To sai na ce wa wata ‘yar uwa ta ni wace sana’a zan yi yanzu, sai ta ce min ai in fara sana’ar Burodi domin su a can Legas sana’ar ta samu karɓuwa sosai. Saboda haka sai na koma na faxa masa cewa zan fara sana’ar Burodi kuma zan koma makaranta, sai na je na nemi takardar neman gurbin shiga Open University dayake babu wahalar samu.

Ana nan sai ‘yar’uwar tawa ta ce min akwai wani mai koyar da gasa Burodi zai shigo Abuja, haka kuwa aka yi kamar da wasa sai ga shi ya zo, sai na yi rajista da shi. Dayake ajin kwana ɗaya ne kawai tun daga safe har zuwa ƙarfe biyar na yamma, duk na yi rajista na yi komai, da lokaci ya yi aka kira ni mu ka je mu ka fara karatun abin gwanin ban sha’awa. Har na fara sayen wani inji na ajiye, daga nan ban sake bi ta kansa ba har kusan shekara guda, sai Baba ya ce “wannan injin kin sayo shi ne kawai ki dinga kallon shi?” Sai na ce mishi a’a. Sai ya ce to in soma domin a fara sani na ko ba don samun riba ba. Haka mu ka fara kamar da wasa, yau mu faɗi gobe mu ci riba har mu ka kawo yanzu.

Ke nan dai idan na fahimce ki kin koyi aikin Burodin ne a cikin rana guda ko kuwa kin ci gaba da koyo?
E kin san idan ki na da sha’awa da ra’ayin abu a ran ki sai ki ga bai zamo wani abin wahalar koyo ba a gare ki; a da babu abin da na fi sha’awa a rayuwa ta irin girka abinci, sai in tsaya in ta kallon wasu abubuwa da su ka shafi girke-girke, kuma ina da sha’awar gasa Burodi. To na je na koya na rana guda sai kuma na cigaba da bibiyar littafi ina karantawa kuma ina yi, sannan wanda ke yi min Burodin shi ma sai mu ka dinga shiga wurin gasawar tare ina ganin yadda ya ke yi, to haka mu ka kama yi.

Waɗanne nasarori ki ka samu zuwa yanzu ta sanadiyyar wannan sana’a ta gasa burodi?
To nasarori kam Alhamdu lillahi, duk da dai ba za a ce mun tara ba, amma dai idan wata matsala ta taso za ka ɗauka ka magance matsalar ka ba tare da tarabbabi ko fargaba ba, idan wani ma ya na neman taimako za ka taimaka masa, za ka yi wa iyayen ka da ‘yan uwanka. Daɗin sana’ar ke nan, kuma duk inda na shiga za ki ji ana Hajiya mai Tara-Tara ko Hajiya mai Burodi ta zo, da wuya ki ji wani ya faɗi suna na. To gaskiya ni dai wannan sana’a ta yi min ko

Mata na fuskantar ƙalubale a harkar sana’a musamman a Arewacin Nijeriya, inda ake yi masu kallon waɗanda ya kamata su zauna a gidajen su su ci gaba da zaman aure da kulawa da ‘ya’yan su. To ke kin fuskanci ƙalubale makamanci haka a cikin sana’ar ki?
To gaskiya ƙalubale iri daban-daban na fuskanta, amma ba irin wannan ba, domin ko a lokacin da zan yi rajista domin samun lambar hukumar NAFDAC na wahala sosai, kuma kin san aikin sana’ar Burodi maza aka san su da ita, da wuya ki ga mace ta na aikin Burodi sai dai idan an yi ta je ta ɗauka, yanzu za ki ga abin da mata ke yi ke nan, amma da wuya ki ga mace tsamo-tsamo ana gasa Burodi da ita.

Hajiya Farida

Kuma sai ƙalubale na biyu kafin Burodin ya samu karɓuwa wajen mutane shi ma na wahala sosai, saboda a lokacin ni ke fita da kaina, in loda Burudo a mota in je wannan unguwa in je waccan, wata rana su ɗauka wata rana su qi amsa, tun mu na rabin buhu har ya zamto yanzu mu na yin buhu bakwai. Sannan kuma ga ɗalubale tsakanin kwastomomi, ga kayan aiki kullum su na ƙara tashi, idan an ƙara wa Burodi kuɗi kwastoma ya yi ƙorafi.

To Hajiya ya maganar iyali?
Ina da yara uku, maza biyu sai mace ɗaya.

Wace shawara za ki bai wa mata, musamman waɗanda su ke zaman jiran sai mazajen su ko iyayen su sun yi masu?
To ni dai ina faɗa wa mata musamman ‘yan matan da za su yi aure ba su da wata sana’ar yi, idan ka tambaye su su ce sun gama makaranta su na jiran aikin gwamnati, sai in ji kamar ni za a kai, domin na san mene ne a cikin gidan auren, rashin sana’ar yi ta na daga cikin abin da ke kawo cikas a aure, saboda yawan ba ni ba ni ɗin nan shi ke jawo rikici da saɓani a cikin gida. Ina ba wa matan aure da ‘yan mata shawara ko da sun kammala makarata kafin su yi aure a ce su na da sana’ar hannu, duk da shi aure havo ne zuwa ya ke yi, amma ki je gidan mijin ki da sana’ar ki ya na da kyau sosai.

Sannan kafin ki fara sana’ar idan ki na gidan iyayen ki ne, sai ki duba ki gani mene ne ba ku da shi a unguwar ku wanda kuma jama’a na buqatar shi amma sai sun fita sun nemo a waje, idan ki na da hali kuma za ki iya yin ta sai ki yi. Idan kuma matar aure ce sai ki duba ki gani ina ki ke zuwa, idan wajen aiki ne sai ki duba ki ga menene mutanen wurin su ka fi so kamar zovo da sauran kayayyaki makamancin su. Ni kin ga kafin in yi aure zoɓo na ke yi in tafi da shi makaranta in je in sayar.

Waɗanne ƙasashe ki ka taɓa zuwa a rayuwar ki?
Na je ƙasar Saudiyya na sauke farali.

Wane kalar abinci ki ka fi so?
To a da lokacin da mutum ya ke yaro idan aka tambaye shi kalar abincin da ya fi so, sai ki ji ya zayyano wancan ya zayyano wancan, amma yanzu ni tun da na fara sana’ar nan wani lokacin ma ba abincin ba ne a gaba na, duk abin da na samu shi zan ci. Amma idan na samu sukuni na koma gida da daddare abin da na ke so in samu in ci shi ne tuwon shinkafa miyar kuka wanda ya ji nama zuƙu-zuƙu, ga ɗan man-shanu da yaji na barbaɗa mishi. Amma bacin wannan kowane abinci na samu zan ci amma da daddare idan na koma gaskiya ina so in ga tuwo a gaba na.

Wane abu ne ya ke saurin ɓata miki rai?
Gaskiya ni dai na tsani in ce ba ni, ka ce ba za ka ba ni ba, saboda kafin in tambaye ka ɗin ma gaskiya da wahala kuma zai ɗauki lokaci, kuma sai dai idan na shiga wata gagarumar damuwa ce wadda babu makawa sai na tambaya xin. Sannan kuma idan mutum ya nemi ya ci mutuncin iyaye na ko ya ƙasƙantar min da su gaskiya nan ne za ki ga ɓacin raina, amma ya na da wahala ki ga raina ya ɓaci.

Ki na da sha’awar siyasa?
Ina da sha’awar siyasa sosai, amma kuma ta na ba ni tsoro; yanayin da na fi so ke nan ma lokacin da aka buga gangar siyasa aka fara kamfe, in zauna ina kallon talabijin ana yaƙin neman zaɓe, wannan ya fito ya yi ta shi ƙaryar wannan ma ya fito. Sannan ga waƙoƙin siyasa kala-kala da ke tashi ta ko’ina. Abin ya na ba ni sha’awa kuma ina jin daɗin yanayin. Saboda haka ina son siyasa sosai.

To ke nan akwai yiwuwar wata rana mu ji ko mu ga hotunan ki a gari an mammanna ki na neman kujerar ’yar majalisa ko shugabar ƙaramar hukuma.
(Dariya) E to, watakila, ba wanda ya san abin da gobe za ta yi sai Allah.

Wane abu ya fi birge ki a rayuwar ki?
Gaskiya ni dai ba ni da wani abu guda ɗaya da zan ce shi ya fi birge ni, kusan duk wani abu da ya ke da kyau ya na birge ni.

Wane kalar kaya ki ka fi sha’awar sanyawa ko ya fi birge ki?
Gaskiya ina son doguwar riga a rayuwa ta, saboda ita ce rigar da mace mai jiki za ta sa ta ɓoye jikin ta ba tare da ta nuna ba, kuma saboda yawanci ba su da nauyi kuma nan da nan za ki shirya ki sanya abin ki. Kuma doguwar rigar kowace kala ina da sha’awa matuƙar za ta yi min kyau a jiki.

To Hajiya mun gode.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *