Rashawa: SERAP ta buƙaci a binciki ɓacewar biliyan N4.4 a Majalisar Tarayya

Ƙungiyar Kare ‘Yancin Zamantakewa Da Yaƙi Da Cin Hanci (SERAP), ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa Dr Ahmad Lawan, da takwaransa na Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila, a kan su buƙaci hukumomin yaƙi da rashawa su binciki badaƙalar ɓatan dabon da kasafin biliyan N4.4 na Majalisar Tarayya ya yi kamar yadda rahotannin binciken ofishin Babban Jami’in Bincike na Ƙasa suka nuna.

A wata wasiƙa da ta samu sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ƙungiyar ta ce, “Ta hanyar kwatanta jagoranci nagari a kan wannan batu, Majalisar Tarayya za ta iya nuna wa ‘yan Nijeriya cewa ɓangaren yin doka na gwamnati, ɓangare ne mai aiki da gaskiya wanda ke kare muradun ‘yan ƙasa da kuma tabbatar da gwamnatin Shugaba Buhari ta sarrafa dukiyar ƙasa ta hanyar da ta dace.”

A cewar SERAP, “Idan majalisar ta magance wannan matsalar bisa adalci yadda ya kamata, hakan zai kore zargin da ‘yan ƙasa ke yi wa majalisar na gazawa wajen sauke haƙƙoƙin da suka rataya a kanta yadda ya dace. Kuma hakan zai tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa da gaske majalisar take yi game da sha’anin yaƙi da rashawa don amfanin al’umar ƙasa.

“Rashawa da karkatar da dukiyoyin ƙasa da aka yi, laifi ne da ya saɓa wa Kundin Dokokin Ƙasa na 1999 (wanda aka gyara), har da abin da ya shafi ƙasa a matakin ƙasa-da-ƙasa.

“Gazawar majalisar wajen yin bincike kan waɗannan zarge-zarge, gano kuɗade da kadarorin da aka wawushe tare da hukunta duk wani da aka samu da hannu cikin badaƙalar, hakan zai sanya guwawun ‘yan ƙasa su yi sanyi game da yardar da suke da ita a kan majalisar.”

Wasiƙar SERAP ta nuna cewa, “A 2015, rahoton Babban Jami’in Bincike ya nuna Majalisar Tarayya ta kashe kuɗi N8,800,000.00 ba a bisa ƙa’ida ba wanda hakan ya saɓa wa dokar kuɗi 710. Haka nan, majalisar ta kashe N115,947,016.00 ba tare da wani bayani a rubuce ba, sannan ta sake kashe N158,193,066.00 tsakanin Janairu da Yunin 2015 babu sahihin bayani”, da dai sauransu.

SERAP ta ce, ta aika kwafin wasiƙar tata ga Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da shugaban hukumar ICPC, Bolaji Owasanoye, haɗa da shugaban riƙo na hukumar EFCC, Mohammed Abba domin su shaida ƙudirinta.