Rashin tsaro: An cafke ‘yan Pakistan 7 a Benuwai, an halaka ‘yan bindiga 6 yayin samame

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Benuwai ta ce ta kama wasu ‘yan ƙasar waje guda bakwai bisa wani shiri mai alamar tambaya ga Nijeriya da kuma Benuwai a keɓance.

Da yake ganawa da ‘yan jarida a Makurɗi, Kwamishinan ‘yan sandan, Cletus Nwaduogbu ya ce tun a ranar 1 ga Yuli ne sashen leƙen asiri na yankin Otukpo ya samu wasu bayanan sirri akan cewa wasu ‘yan wajen sun kama waje a wani otal, inda a wani samame aka gano ‘yan Pakistan guda bakwai, waɗanda suka gaza bayar da bayanan iƙirarinsu na cewa su masu aikin lantarki ne.

Ya ce, sun shigo Nijeriya ne daga mabambanta ƙasashe gabanin su haɗe a Legas, salon da masu aikata miyagun laifuka suke amfani da shi.

Ya bayyana cewa, bayan kamen ne kuma aka garzaya da su Abuja domin cigaba da gudanar da bincike akansu bisa zargin su da hannu a ayyukan ta’addanci.

A wani labarin kuwa, rundunar ta halaka wasu ‘yan bindiga guda huɗu a ranar 2 ga Yuli a maɓoyarsu da ke Seyoo Gbajimba a Ƙaramar Hukumar Guma, inda suka ƙwato makamai da suka haɗa da bindigar AK-47, alburusai shida da wayoyin hannu da wasu kayan tsafi.

A ranar ne kuma jami’an na Sashen B suk ƙwato wasu bindigogi ƙirar pistol guda huɗu da aka ƙunshe a wata jarkar baƙin mai a wata motar Sharon da ta taho daga Ayingba na Jihar Kogi bayan wanda ake zargin ya tsere daga tashar mota.

By Babaji