Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce amfani da ƙarfin soji kaɗai ba zai kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya ba, inda ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar gwamnati, jami’an tsaro da al’umma wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen taron tsaro na Arewa ta Tsakiya na shekarar 2026 da aka gudanar a Makurdi, Jihar Benue, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilce shi.
Ya ce rashin tsaro ya zama matsala mai sarƙaƙiya da ba wata hukuma, wani matakin gwamnati ko wata al’umma guda ɗaya za ta iya magancewa ita kaɗai ba, musamman ganin yadda masu aikata laifuka ke ƙetare iyakokin jihohi da ƙananan hukumomi.
“Babu wata hukuma guda ɗaya, ko wani matakin gwamnati guda ɗaya, ko wata al’umma guda ɗaya da za ta iya tabbatar da tsaron wannan yanki ita kaɗai,” inji shugaban.
Tinubu ya ce ƙarfin soji na iya daƙile tashin hankali, amma ba zai iya magance ƙorafe-ƙorafen da ke haifar da rikice-rikice ba.
Ya bayyana rigingimu kan filaye da ruwa, sauyin yanayi, kwararowar hamada, taƙaddamar amfani da ƙasa, raunin hanyoyin sasanta rikice-rikice da yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ke ƙara rura wutar rikici.
Shugaban ya buƙaci shugabannin gargajiya da na addinai su taka muhimmiyar rawa wajen samar da bayanan sirri tun da wuri, tare da sasanta rikice-rikice a tsakanin al’umma.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanan da suka dace kan ayyukan masu aikata laifuka, tare da guje wa kare su saboda zumunci, ƙabila ko wata manufa.
Tinubu ya ce mata da matasa ma suna da muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, yana mai cewa gwamnati za ta ƙara samar da damammakin tattalin arziki da ayyukan yi domin rage wa matasa sha’awar shiga miyagun laifuka.
Ya kuma buƙaci ’yan kasuwa da abokan hulɗar ci gaba su ƙara saka hannun jari a yankin, yana mai cewa bunƙasar tattalin arziki na taimakawa wajen samar da tsaro mai ɗorewa.
“Zaman lafiya da saka hannun jari suna ƙarfafa juna. Kowace masana’anta da aka gina, kowace gona da aka faɗaɗa da kuma kowane matashi da aka samar wa aikin yi, gudummawa ce ga tsaron yankin,” inji shi.
Tinubu ya kuma umarci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, da ya miƙa masa shawarwarin da aka cimma a taron.
Ya kuma buƙaci a sanya wa kowace shawara wanda zai ɗauki alhakin aiwatar da ita, tare da kayyade wa’adin aiwatarwa da kuma hanyoyin auna nasarar da aka samu.
