Gwamnatin Tarayya ta umarci jami’o’i, kwalejojin fasaha da ilimi su shiga tsarin bada matsayi na ƙasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayar da umarnin shiga cikin tsarin tantancewa da tsara matsayin manyan makarantun ilimi na ƙasa ya zama wajibi ga dukkan jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi da ke faɗin ƙasar.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja, yayin wata ganawa da Kwamitin Ba da Shawara kan Matsayin Jami’o’in Nijeriya, wanda aka faɗaca aikinsa tare da sauya masa suna zuwa Kwamitin Ba da Shawara kan Matsayin Manyan Makarantun Ilimi na Nijeriya.

A cewar wata sanarwa da Ikharo Attah, Mai Ba Ministan Ilimi Shawara kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, ya fitar, faɗaɗa tsarin tantancewar na da nufin inganta ingancin ilimi, daƙile rashin ɗaukar alhaki, ƙara ƙwarewar cibiyoyin ilimi da kuma taimaka wa manyan makarantun Nijeriya su yi gogayya a matakin duniya.

Alausa ya ce, tsarin zai bai wa manyan makarantun ilimi ma’aunin da za su riƙa amfani da shi wajen auna yadda suke gudanar da ayyukansu, gano matsalolin da ke kawo cikas ga ci gabansu da kuma bibiyar irin ci gaban da suke samu. Ya ƙara da cewa, hakan zai kuma taimaka wajen ƙarfafa kyakkyawar gasa tsakanin cibiyoyin ilimi domin kowacce makaranta ta ƙara ƙoƙarin inganta ayyukanta.

A ƙarƙashin sabon tsarin, za a riƙa tantance jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi bisa tsarin matsayi guda na ƙasa. Gwamnatin Tarayya ce za ta ɗauki nauyin gudanar da aikin ta hannun Asusun Tallafawa Manyan Makarantun Ilimi (TETFund).

Ministan ya bayyana cewa za a fara aikin tantance matsayin jami’o’i na shekarar 2026/2027 a watan Satumba, yayin da kwamitin zai tsara lokacin da za a faɗaɗa aikin zuwa kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi. Ya ce gwamnati za ta samar da ƙa’idojin da za su mayar da tsarin na dindindin, sannan ta sanar da shugabannin jami’o’i da sauran manyan makarantun ilimi a hukumance cewa shiga cikin tsarin zai zama wajibi.

Alausa ya bayyana cewa wannan manufar na daga cikin sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a fannin ilimi ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta hanyar Shirin Farfaɗo da Bangaren Ilimi na Nijeriya. Ya kuma tabbatar da cewa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya za ta samar da jagorancin manufofi, kuɗaɗen gudanarwa da horar da ma’aikata da ake buƙata domin tabbatar da cewa tsarin tantance matsayin cibiyoyin ilimin ya kasance abin dogaro, mai ɗorewa kuma mai tasiri.

A cewarsa, ma’aikatar za ta yi aiki tare da kwamitin wajen shirya horon ƙarin ƙwarewa ga ma’aikatan da ke aiki a cibiyoyin ilimi, da kuma shirye-shiryen inganta ƙwarewar manyan makarantun ƙasar.

Manufar hakan, inji shi, ita ce ƙara wa cibiyoyin ilimi ƙarfin gudanar da ayyukansu da kuma ƙara yawan jami’o’in Nijeriya da sauran manyan makarantu da za su samu karɓuwa a matakin duniya.

By ukarofi