Nijeriya ba ta da shirin ƙera makaman nukiliya – Jimoh Ibrahim ga Majalisar Dinkin Duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Jakadan Nijeriya a Majalisar ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya bayyana cewa Nijeriya ba ta mallaki makaman nukiliya, kuma ba ta taɓa gudanar da wani shiri na ƙera makaman nukiliya ba. Ibrahim ya ce, Nijeriya na ci gaba da nuna ƙudurinta na goyon bayan ƙoƙarin ƙasashen duniya na kawar da gwaje-gwajen makaman nukiliya baki ɗaya.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a gaban Babban Taron Majalisar ɗinkin Duniya a birnin New York a yayin taron cikakken zama na 108 na zaman karo na 80 na majalisar.

Ibrahim, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar ɗinkin Duniya kan Kasafin Kuɗi da Gudanarwa, ya yi amfani da damar wajen yin kira da a sake duba Mataki na 2(7) na Yarjejeniyar Kafa Majalisar ɗinkin Duniya.

Ya ce ƙa’idar da ta hana Majalisar ɗinkin Duniya tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasashe bai kamata ta zama shinge ga ɗaukar matakin ƙasa da ƙasa kan ƙasashen da ke gudanar da gwaje-gwajen makaman nukiliya ko kuma mallakar makaman ƙare dangi ba.

Jakadan, wanda ya gabatar da matsayin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce Nijeriya na da muhimman hukumomi da tsare-tsaren sa ido da kuma hanyoyin tsara dokoki domin bibiyar al’amuran da suka shafi makaman ƙare dangi.

Ya bayyana Hukumar Makamashin Nukiliya ta Nijeriya (Nigeria Atomic Energy Commission) a matsayin zaya daga cikin muhimman hukumomin da ke da alhakin kula da ayyukan da suka shafi nukiliya da kuma tsarin dokokin da ke jagorantar su a ƙasar. A cewarsa, Nijeriya na yin haɗin gwiwa da ƙasashe daban-daban a duniya, ciki har da Rasha, Chana, Faransa, Koriya ta Kudu da Amurka, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Ibrahim ya ce Shugaba Tinubu ya umurce shi da sake tabbatar da shirye-shiryen Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin ganin an kawar da gwaje-gwajen makaman nukiliya daga tsarin duniya. Ya kuma ce Nijeriya ta goyi bayan matsayar da ƙungiyar ƙasashen Afirka ta gabatar, tare da taya ƙasashen duniya murnar cika shekaru 30 da aka kafa Yarjejeniyar Hana Cikakken Gwajin Makaman Nukiliya (CTBT).

Jakadan ya bayyana cewa Afirka na ci gaba da kasancewa nahiya da ba ta yarda da mallakar makaman nukiliya ba, tare da kin amincewa da gwaje-gwajen abubuwan fashewar nukiliya a faɗin nahiyar.

Saboda haka, ya yi kira ga ƙasashe mambobin Majalisar ɗinkin Duniya da su ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na kawar da gwaje-gwajen makaman nukiliya. Ya ce ɗaukar irin wannan mataki na da matuƙar muhimmanci wajen samar da duniya mafi aminci da kuma kawar da barazanar da makaman nukiliya ke haifarwa ga bil’adama.

Ibrahim ya kuma taya aasashe mambobin Majalisar ɗinkin Duniya murnar irin ci gaban da aka samu cikin shekaru 30 da suka gabata wajen yaƙi da gwaje-gwajen makaman nukiliya a duniya.

By ukarofi