Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Legas ta gargaɗi mazaje kan tilasta wa matansu yin jima’i ba tare da yardarsu ba, tana mai cewa duk mutumin da ya aikata hakan na iya fuskantar hukuncin ɗaurin rai da rai.
Daraktan Shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Legas, Adebayo Harow, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin wani taron manema labarai na ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a kan Rigakafi Cin Zarafin Gida (DSɓA) na jihar.
Yayin da yake amsa tambaya kan ko dokokin Nijeriya sun bai wa matar aure damar kai ƙarar mijinta bisa zargin fyaɗe idan ya yi lalata da ita ba tare da yardarta ba, kamar yadda ake yi a wasu ƙasashe, Harow ya ce dokar Nijeriya ba ta ɗauki irin wannan a matsayin fyaɗ ba. Sai dai ya ce dokar Jihar Legas ta sanya irin wannan aiki ƙarƙashin laifin “cin zarafi da jima’i ta hanyar tilas”, wato Seɗual Assault by Penetration, wanda hukuncinsa zai iya kai wa ɗaurin rai da rai.
Harow ya ce, idan ma’aurata sun samu matsala a tsakaninsu, matar kuma ta ƙi yarda da kwanciyar aure da mijinta, ba shi da ikon tilasta mata. Ya ce idan ya tilasta mata sannan ta kai rahoto, ba za a tuhume shi da laifin fyaɗe ba, sai dai da laifin cin zarafi da jima’i ta hanyar tilas, wanda ke da hukuncin ɗaurin rai da rai a ƙarƙashin dokar jihar.
“Duk mutumin da yake ganin cewa saboda ya biya sadakin matarsa, babu wanda zai iya ɗaukar mataki a kansa idan ya aikata mata cin zarafin gida, ya kamata matar ta kai rahotonsa ga Hukumar Yaƙi da Cin Zarafin Gida da Jima’i. ƙarƙashin dokar laifuka ta Jihar Legas, ba za a iya zargin mutum da yi wa matarsa fyaɗe ba muddin suna tare kuma babu wata matsala a tsakaninsu.
“Amma da zarar wata matsala ta shiga tsakaninsu, matar kuma ta ƙi yin jima’i da shi, mijin ba shi da ikon tilasta mata. Idan ya tilasta mata kuma ta kai rahoto, ba za mu tuhume shi da fyaɗe ba, sai dai da cin zarafi da jima’i ta hanyar tilas, kuma hukuncinsa ɗaurin rai da rai ne,” inji shi.
