Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur A Cikin Ruwa ta Nijeriya (NUPRC) ta yi gargaɗin cewa babu wani sabon kuɗin aiki, haraji ko caji da ya shafi ayyukan ɓangaren haƙo ɗanyen mai da ya kamata a ƙaddamar ba tare da an fara tuntuɓar hukumar da sauran masu ruwa da tsaki ba.
Hukumar ta ce, babu wani sabon caji ko sauya adadin kuɗin da ake karɓa da ya shafi harkokin man fetur da ya kamata a fara aiwatar da shi ba tare da an fara tuntuɓar NUPRC da sauran masu ruwa da tsaki ba.
NUPRC ta bayyana hakan ne a wata takardar sanarwa mai kwanan wata 28 ga Agusta, 2026, wadda aka aika wa masu gudanar da ayyukan man fetur, masu lasisi, masu hayar wuraren haƙo mai da kuma kamfanonin da ke ba su kulawa.
Shugaban Hukumar NUPRC, Oritsemeyiwa Eyesan, ne ya sanya hannu kan takardar, bayan kammala aikin wani kwamitin bincike na ma’aikatar da ya duba batun harajin jirage masu saukar ungulu kan ayyukan zirga-zirgar jiragen sama.
Hukumar ta ce, kwamitin ya yanke shawarar cewa daga yanzu, duk wani sabon kuɗin sabis, haraji ko caji, ko kuma ƙarin da aka yi wa wani caji da ke shafar harkokin man fetur na cikin ruwa, dole ne ya kasance an fara tattaunawa da NUPRC da sauran hukumomin da abin ya shafa.
NUPRC ta ce ta kafa wannan matsaya ne bisa Sashe na 25 na Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 (PIA).
Wannan mataki ya biyo bayan cece-kuce da ya taso kan ƙaddamar da harajin jirage masu saukar ungulu, wanda ya kai ga kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi domin duba matsalolin da harajin ya haifar.
Kwamitin ya ƙunshi wakilan Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya, Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Nijeriya (NAMA) da kuma kamfanin da NAMA ta ɗora wa alhakin karɓar kuɗin harajin.
NUPRC ta ce harajin dala 300 kan kowace saukar jirgin sama mai saukar ungulu zai ci gaba da aiki. A cewar hukumar, za a ci gaba da biyan kuɗin ne ga Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Nijeriya (NAMA) ta hanyar tsarin karɓar kuɗaɗen da ta amince da shi.
Sai dai NUPRC ta fayyace cewa Terminal Naɓigational Charge (TNC), wato kuɗin kula da zirga-zirgar jiragen sama a tashoshin saukar jirage, ba ya shafar wuraren saukar jirage masu zaman kansu da ke cikin teku.
Hukumar ta ce, TNC zai shafi saukar jirgi ne kawai a filin jirgin sama mallakar gwamnati, ba kuma wuraren aiki ko dandamalin kamfanonin man fetur da ke cikin teku ba. Sai dai cajin zai ci gaba da aiki ga ayyukan jirage masu saukar ungulu da ba su da alaƙa da harkokin haƙo ɗanyen mai, kamar kwashe marasa lafiya ta jirgi, hayar jirgi na musamman da ayyukan noma.
Hukumar ta ce za a ɗauki harajin a matsayin kuɗin doka da ake biya kan ayyukan zirga-zirgar jiragen sama, kuma za a yi amfani da shi wajen tsara rahotannin kuɗaɗen kamfanonin da abin ya shafa.
NUPRC ta ce za ta fitar da ƙarin bayani kan yadda kamfanonin za su ware da kuma bayyana waɗannan kuɗaɗe a cikin rahotannin kuɗinsu. Hakan ya haɗa da yadda za a yi da kuɗaɗen TNC da wasu kamfanonin suka riga suka rubuta a matsayin kuɗin da suka kashe wajen ayyukan jirage masu saukar ungulu na harkokin man fetur.
NUPRC ta kuma bayyana cewa an umarci NAMA da ta ƙara samar da na’urorin sa ido da bibiyar jiragen da ke tashi a ƙananan tsawo, domin ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta kula da sararin samaniyar Nijeriya.
A cewar hukumar, wannan tsarin zai buƙaci kamfanonin da abin ya shafa su samar da bayanan jiragen da suka tashi, bayanan motsin jirage da kuma bayanan ayyukan da suke gudanarwa a teku. Sai dai NUPRC ta ce NAMA ce za ta sanar da kamfanonin takamaiman bayanan da ake buƙata, kasancewar wannan na daga cikin nauyin da doka ta ɗora mata.
A ƙarshe, NUPRC ta buƙaci masu gudanar da harkokin man fetur na sama, masu lasisi, masu hayar wuraren aiki da kuma kamfanonin da ke ba su sabis na jirage masu saukar ungulu da su bi sabon tsarin. Hukumar ta kuma umarce su da su daidaita yarjejeniyoyin kasuwanci, takardun neman biyan kuɗi da tsarin dawo da kuɗaɗen da suka kashe daidai da matsayar da aka cimma.
